Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya kai wa Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ziyarar Sallah a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mataimakin shugaban kasar da ya isa Sakkwato tare da gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da sauran ‘yan siyasa, ya jaddada bukatar shugabannin Arewacin Nijeriya su hada kai domin ganin an magance matsalolin da suka addabi yankin.
- JKS Tana Da Mambobi Sama Da Miliyan 98 Ya Zuwa Karshen 2022
- Kura Ta Turnike Majalisar Dattawa Kan Nadin Shugaban Marasa Rinjaye
Ya ce, “Ba za a iya samun zaman lafiya a cikin yanayin tashin hankali ba, don haka ya kamata shugabannin yankin su tabbatar sun yi aiki tare domin samun zaman lafiya a yankin.
“Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za ta bai wa sarautun gargajiya irin karramawa da girmamawa da suka dace.”
Da yake mayar da martani, Sarkin Musulmi ya gargadi ‘yan Nijeriya kan bukatar yin aiki tare domin samun zaman lafiya da hadin kan kasa.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nuna fahimta tare da bai wa sabuwar gwamnati dama musamman sabbin sauye-sauye don samu sakamakon sabbin manufofin gwamnati.
A baya dai mataimakin shugaban kasar ya yi wata ganawar sirri da gwamna Ahmed Aliyu, a gidan gwamnati, kafin ya wuce fadar.