Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai bar Abuja zuwa birnin Dallas na kasar Amurka, domin ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN), ya ruwaito cewa, hukumar kula da harkokin Afirka ce ta shirya taron.
- Shettima Ya Kaddamar Da Kwamitin Mutum 37 Kan Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashi
- Na Yaba Da Yadda Aka Bai Wa Mutum 100 Lambar Yabo A Kano – Kashim Shettima
Mista Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Nkwocha ya ce Shettima zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da na ‘yan kasuwa a fadin Afirka da Amurka a wajen halartar taron.
A cewarsa, taron zai kunshi tattaunawa kan harkokin kasuwanci da sada zumunta wanda aka shirya gudanarwa a Cibiyar Taro ta Kay Bailey Hutchison a Dallas, Texas.
Ya ce shugabannin Afirka da ake sa ran a taron sun hada da, shugaban kasar, Jamhuriyar Laberiya; Joseph Boakai da shugaban kasar Malawi; Lazarus Chakwera da shugaban kasar Angola, Joao Lourenço.
Nkwocha ya ce, sauran shugabannin Afirka da za su halarci taron sun hada da shugaban kasar Botswana, Mokgweetsi E. K. Masisi da shugaban kasar Cabo Verde, José Maria Neves, da mataimakin firaministan kasar Lesotho, Nthomeng Majara.
Ya ce baya ga zaman taron kolin, Shettima zai yi jawabi a wani taro kan zuba hannun jari a Afirka.