Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. ‘Yan’uwa Musulmi, barkanmu da kara saduwa a wani mako a cikin filinmu albarka. Da yake aikin Hajjin bana yana kara karatowa, mun dakatar da sakonni a kan darussan Tafsir na Ramadan sai zuwa wani lokaci in sha Allahu za mu ci gaba, amma daga yanzu za mu mayar da hankali a kan bayanin aikin Hajji zuwa abin da ya sauwaka kamar yadda muka taba kawowa a wannan Shafin a wasu shekarun baya.
Aikin Hajji ibada ne da yake da lokaci kebantacce da wuri kebantacce da ake gudanarwa. Ma’ana ba a ko wane lokaci ko wurin da mutum ya ga dama ne ba zai ce zai yi Hajji. Akwai lokaci da wurin da Allah ya kebance su da Hajjin.
- Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
- Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
Lokaci (na zamani) da ake Hajji shi ne wata guda uku, Shawwal, Zhul-kiyda, Zhul-hajji, su ne kuma ake kira da Mikati zamani. Allah (SWT) ya ce a cikin Alkur’ani: “Suna tambayar ka game da wadannan jirajiran wata, ka ce lokuta ne na mutane da suke ibadodinsu.” Don haka da zarar watan Shawwal ya kama, to an shiga lokacin da mutum zai iya yin harama da Hajji.
A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana. Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba.
Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana da wuraren da Shari’a ta kebance don yin harama da shi. Duk wanda zai yi Hajji ko Umura, bai halasta gare shi ya tsallaka wadannan wuraren ba tare da ya yi harama ba.
Manzon Allah (SAW) ya sanya wa ko wadanne mutane wurin da za su yi harama (Mikati). Ya sanya wa mutanen Madina Zhal-hulaifa ya zama wurin haramarsu. A yanzu ana kiran wurin da sunan Abaru Ali. Haka nan sauran mutanen duniya da suka fara wucewa Madina ziyarar Annabi (SAW) daga ko ina a duniya, idan za su dawo Makka yin Hajji ko Umura su ma a nan Zhal-hulaifa za su yi harama. Ba za su ce sai sun koma Mikatinsu ba da aka sanya musu. Wurin yana nan daga Arewacin Madina kuma tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 450 ne, kusan shi ne mafi tsawo daga Makka a cikin sauran wuraren haramar Hajji.
Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Sham (Siriya) da sauran kasashe irin su Palasdin da Urdun wurin da ake kira Juhufa ya zama wurin haramarsu. Wurin yana nan a arewa-maso-yammacin Makka kusa da Radiga wadda Hausawa suke kira da Radinga. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 187. Amma tunda ruwa ya shafe Juhufa a halin yanzu, Radiga ce ta zama wurin haramar su mutanen Sham da Misra da sauran wadanda suka bi ta wajen, ita kuma tsakaninta da Makka tafiyar kilomita 204. Muma mutanen Nijeriya nan ne Mikatinmu da sauran mutanen kasashen da za su bi wurin, kamar na Yammacin Afirka.
Su kuma mutanen Najadu, Annabi (SAW) ya sanya musu Karnul-manazil ya zama Mikatinsu. Wani dutse ne da ke gabashin Makka yana kallon Arfa. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94.
Su kuwa mutanen Yemen, Annabi (SAW) ya sanya wa mutanensu Yalamlam ya zama Mikatinsu. Shi ma dutse ne da ke kudancin Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 54.
Annabi (SAW) ya kafa wa mutanen Iraki Zatu’irkin a matsayin Mikatinsu. Wuri ne da yake arewa-maso-gabas din Makka. Tsakaninsa da Makka tafiyar kilomita 94, nisan shi da Makka daya ne da na Mikatin mutanen Najadu.
Wadannan wurare da Annabi (SAW) ya kafa, su ne wuraren da mutanen duniya za su yi haramar Hajji ko Umura.
Idan zuwa Hajji ko Umura ya kama mutum a wata kasar da ba tashi ba, zai yi amfani ne da Mikatin da mutanen wannan kasar suke yin harama, ba zai ce tunda shi ba dan kasar ne ba, sai ya koma ta Mikatin kasarsa, a’a, zai yi haramar ce a Mikatin ‘yan kasan, ma’ana kamar shi ma ya zama dan kasar ke nan.
Amma su kuma wadanda suke cikin Makka (baki da ‘yan garin), a nan cikin garin ne za su yi harama. Kamar misali wadanda suke Hajjin Tamattu’i, bayan sun kammala Umura, to idan ranar da za a yi haramar Hajji ta zo, tun daga gida za su yi harama ba sai sun je wani wuri ba.
Amma idan dan cikin Makka zai yi Umura bayan Hajji, sai ya fita zuwa Tan’im kafin ya yi harama kamar yadda Annabi (SAW) ya yi umurni a kai Ummul-Mu’umina Aisha (RA) ta yi haramar Umura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp