Assalamu alaikum. Malam don Allah tambaya nake da ita kamar haka: Abaya da mata suke sanyawa tana iya daukan hukuncin Hijabi ne, domin za ka ga ko harami za ka gan su da irin wannan shigar, kuma na yi kokarin leka wasu littafai masu alaka da hijab ban iya kaiwa ga magana a kan hakan ba.
Malam ko akwai maganganun malamai a kai? Allah ya saka maka da alkhairi.
Wa alaykumus salam, To dan’uwa, abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne: ta sanya tufan da zai suturce jikinta, in ban da fuska da tafin hannu a wajan wasu malaman, wasu malaman kuma suna ganin fuska al’aura ce, don haka ita ma ya wajaba a rufe ta, tun a nan kyawun mace yake, kayan da za ta sa su zama masu kauri, ba ya halatta ta yi ado in ba a cikin gidan mijita ba, ko tare da muharramanta.
Suturar mace musulma ba a so ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba a so su zama kayan da za su ja hankali, ko wadanda aka fesa musu turare, mutukar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata, ba ta matse shi ba, za ta dauki matsayin hijabin da Allah da manzonsa, suka yi umarni.
Don neman karin bayani duba: Majmu’ul-fataawa 22\110 da Hijabul-mar’atulmuslima shafi na: 54 zuwa 67.
Allah ne mafi sani.
Ya Halatta Mace Ta Yi Yawo Babu Dankwali A Tsakar Gida?
Assalamu alaikum, Allah gafarta malam shin zan iya yawo a cikin gida ba dankwali a matsayina na mace?
Wa alaikum assalam. Mace za ta iya yawo babu dankwali idan tana tsakanin ‘yan’uwanta mata musulmai saboda al’aurar mace ga ‘yar uwarta mace musulma tana kasancewa ne tsakanin guiwa zuwa cibiya, mutukar akwai mazan da ba muharramai ba to bai halatta ta bude kanta ba, saboda dukkan mace Al’ura ce in ban da fuska da tafukan hannu.
Allah ne mafi sani.