Jama’a barkan ku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a inda a yau shafin namu zai karkata zuwa ga Goron Sallah kashi na biyu, mun kawo muku sakonnin gaishe-gaishen ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa wadanda aka turo.
Sai dai kuma za mu tsakuro kadan daga cikin sakonnin, kafin mun je ga karanto sakon masu karatu sai na fara mika tawa gaisuwar sallah zuwa ga daukacin al’ummar musulmi baki daya ina yi wa kowa barka da sallah da fatan an yi sallah lafiya, musamman Editana Abdulrazak Yahuza Jere tare da iyalansa baki daya, da kuma daukacin ma’aikatan wannan gida na Jaridar LEADERSHIP Hausa, ina yi muku Barka da Sallah tare da Barka da Juma’a da fatan kowa ya yi Sallah lafiya, kuma za a yi Juma’a lafiya.
Yanzu kuma zan je ga sakonnin masu karatu kamar haka;
Sako daga 0701 304 0786:
Assalamu Alaikum ya ku ‘yan uwa musulmi da abokan arziki, ina myku barka da Sallah da fatan an yi Sallah Lafiya, Allah ka nuna ta shekara mai zuwa wassalam.
Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08164205067:
Assalamu alaikum. Gaisuwar Goron Sallah ga mai girma tsohon shugaban hukumar DSS na kasa Alh. Lawal Musa Daura, da mai girma Sani Musa da mai girma shugaban karamar hukumar Daura Alh. Bala Musa da Alh. Akarimukallahu Mal. Zakari Musa da Alh. Aduwa Musa Da Alh Sagir Musa da fatan Allah ya kare su daga sharrin abokan halitta Mutum ko Aljan da fatan za su yi Juma’a lafiya, Allah ya sa haka amin. Ina gaida mai girma Subeb Ciyaman na Jihar Katsina Alh.Lawal Buhari Daura da mai girma ES na Daura Alh. Nura Lawal mai girma Hedimastan Pilot firamare School Tudun Wada Daura Alh. Sani Mamman da Mal. Musa da Mal. Sabiu da Mal. Habu Popula da Mal. Mustapha 1 da Mal. Mustapha 2 da Mal. Hamisu da Malama Fatima Bashar da Malama Amina da Malama Hajara da Malama Sa”ade da Uwata Malama Hajiya Zilai da Malama Habiba Nura Lawal da Mal. Sade da Mal. Abdulhadi 1 da Mal. Abdulhadi 2 da Alh. Mal. Amadu Sabi’u da fatan an Sallah lafiya kuma za a yi Juma’a lafiya.
Sako daga Abubakar Mustapha Jihar Yobe:
Ina yi wa al’ummar musulmai barka da sallah da fatan an yi sallah lafiya, Allah ya karbi ibadunmu. Ina gaida Sulaiman Adamu Tandari Potiskum, Buhari Yahaya Nguru, Ibrahim M. Abubakar Maiduguri, Mutawakkil Gambo Doko, Ashiru Usman sabuwar Gwaram, Ahmadu Abacha Machina, Usman Muhammad Maiduguri, Ibrahim Adamu Mai Azurfa, Abdullahi Saleh Fika, Musa G Usman Damaturu, da fatan sun yi sallah lafiya.
Sako daga Abubakar Mustapha Jihar Yobe:
Assalamu alaikum ina yi wa kowa barka da juma’a Allah ya karbi ibadunmu, ina gaida Nasiru Shehu Yunusari, Manman a maje, Goni Sanda Yunusari, Ibrahim Adamu Mai Azurfa, Idris M. Idris damaturu, Nasiru Kainuwa Hadejia, Kinunu Sani Yunusari, Haruna Muhammad Katsina, Muhammad Maitela, Usman Muhammad Maiduguri, Comrd Ibrahim musa Maiduguri, Ahmad Sulaiman Bajoga, Muhammad Sadi Dan Hausa Baturia, Muhammad Abdulsalam, da fatan za su yi juma’a lafiya.