Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fara kakar wasa ta bana tare da sabon gogaggen dan wasa cikin jerin sunayen ƴan wasansu bayan da suka kara Kylian Mbappé a cikin tawagar kungiyar sai dai kuma hakan bai sa kungiyar ta samu nasara ba a wasanta na farko da Real Mallorca.
Real Madrid za ta nemi maimaita nasarar da ta samu a kakar wasan da ta gabata inda kungiyar ta lashe gasar La Liga da kuma Champions League kuma an ga anfanin hakan bayan nasara a kan Atalanta da ci 2-0, inda ta lashe kofin Uefa super cup, kuma Mbappe ya ci wa kungiyar kwallonsa na farko.
- Mutum Miliyan 7.9 Da Ta’addanci Ya Tagayyara A Jihohi 3 Na Bukatar Agaji – UNOCHA
- An Samar Da Naira Biliyan 2.5 Don Bunkasa Ma’adanai A Nijeriya
Zakarun na nahiyar turai sun kara wa tawagarta karfi da ƴan wasa biyu a wannan bazarar bayan ta kammala daukar Kyllian Mbappé daga Paris Saint-Germain da kuma Endrick Felipe daga Palmeiras ta Brazil.
Amma har yanzu wasu suna ganin Real Madrid za ta sha wahala a wannan kakar saboda ritayar da dan wasa Toni Kroos ya yi a karshen kakar da ta gabata bayan ya taimaka wa kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun turai a watan Yuni.
Toni Kroos ya rataye takalman wasansa ya kuma bar Ancelotti da babban gibi a tsakiya. Haka kuma kyaftin Nacho, wanda ya bar kungiyar zuwa Al-Kadisiyah, sai kuma dan wasan gaba Joselu, wanda ya koma kungiyar Al-Gharafa ta kasar Katar.
Sai dai ganin yadda sauran kungoyoyin La Liga ke shirin tunkarar kakar wasan bana, ba abin mamaki ba ne idan kungiyoyin Barcelona da Atletico Madrid suka takawa kungiyar burki wajen lashe gasar Laliga ta bana.
Barcelona – wadda ita ce babbar abokiyar hamayyar Real Madrid ana ganin akwai alamun rauni ganin yadda ta shiga rudani a kasuwar cinikin ‘ƴan wasa na bazarar nan, inda ya zuwa yanzu take kai wa da kawowa wurin neman ƴan wasan da za ta dauko domin kara wa tawagarta karfi.
A yanzu ɗan wasa mai armashi daya tilo da Barca da dauka shi ne Dani Olmo, duk da daukar lokaci da aka yi ana danganta kungiyar da dan wasan kungiyar Athletico Bilbao, Nico Williams, wanda ya taimaka wa Spaniya ta lashe kofin nahiyar turai a Jamus.
Ita kuwa Atlético Madrid ta yi manyan sauye-sauye a tawagarta inda ta sallami Albaro Morata ta kuma maye gurbinsa da Julian Albarez daga manchester City sai kuma dan wasa Conor Gallagher da kungiyar ta dauka daga Chelsea.
Ita kuma Girona da ta samu tagomashi a bara ta sallami ‘ƴan wasanta da dama da suka taka mata rawar gani a kakar wasan amma kungiyar ta dauki Donny Ban de Beek daga Manchester United da wasu ‘yan wasan a Spaniya.
A Real Madrid, a bangaren mai tsaron raga, Thibaut Courtois ya taka rawar gani a wasannin share fage na wannan bazarar tunda bai je gasar nahiyar turai ba da Belgium, duk da kokarin da Andriy Lunin ya yi a bara, ana sa ran dan wasan na Belgium zai kasance zabin farko na Carlo Ancelotti.
A masu tsaron baya, tafiyar Nacho na nufin cewa Éder Militão na shirin komawa matsayinsa na mai tsaron baya na tsakiya tare da Antonio Rüdiger amma ana ganin akwai bukatar kungiyar ta sayi wani dan wasan bayan ta kara. Amma kungiyar ta so daukar Leny Yoro, wanda ya koma Manchester United.
Yin ritayarToni Kroos ta bar babban gibi amma ana ganin wanda zai ci gajiyar hakan shi ne Eduardo Camabinga, wanda ya samu damar buga wasanni da dama a kakar wasan da ta gabata, kodayake Luka Modrić shi ma zai taka muhimmiyar rawa sakamakon gogewar da yake da ita wanda zai taimaka matuka a wasu wasannin.
Zuwan Kylian Mbappé na nufin cewa dole ne kociyan kungiyar Carlo Ancelotti yasan yadda za a yi a yi wa dan wasan waje saboda ana ganin Rodrygo Goes zai iya komawa benci, idan aka yi duba da irin hazakar Binícius Júnior da Jude Bellingham.
Duk da haka ana ganin mai tsaron raga Andriy Lunin zai iya ficewa daga kungiyar domin neman gurbin buga wasa a wata kungiya, wanda hakan ka iya bude kofa ga yuwuwar dawowar dan wasan aro na bara, Kepa Arrizabalaga daga Chelsea.
Amma kuma duk da haka ana ganin Barcelona da Atletico Madrid ba za su yi kara a gwiwa ba wajen ganin sun lashe gasar ta bana saboda wasan farko ma da Real Madrid ta buga canjaras ta buga, wanda hakan yake nuna cewa akwai babban aiki a gaban kociyan kungiyar, Carlo Ancelotti.