ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Batun Kare Hakkin Bil Adama Makami Ne Kawai Na Dakile Ci Gaban Wasu Kasashe?

by CGTN Hausa
2 years ago
Bil Adama

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Rikici tsakanin Isra’ila da Palasdinu ba sabon abu ba ne ga al’ummar kasa da kasa, amma kuma abu ne na tayar da hankali ganin yadda ake ta gadon rikicin daga zuri’a zuwa zuri’a tamkar wata al’adar gargajiya. Rikici da mace-mace batu ne da bai kamata duniya ta lamunta ba, haka kuma batu ne dake bukatar a lalubo bakin zaren warware shi tun daga tushe.

A ranar Lahadi, ofishin manyan jami’an MDD mai kula da hakkokin bil adama ya ce yanayin keta hakkin bil adama a Zirin Gaza na kara tsananta, yana mai cewa matakin Isra’ila sun sabawa dokar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa. Sai dai maimakon a ji kasashen duniya dake ganin kansu a matsayin manya kuma masu fada a ji suna daga murya game da hakan, shiru ka ake ji, sai ma kokarin da suke yi ta kowacce hanya na karawa mai cin zali karfi wajen ci gaba da aikata mummunan aikin da galibin kasashen duniya ke tir da shi. Yadda ake yayata batun kare hakkin bil adama a baki, ya bambanta da aiwatar da shi a aikace. Mun ga yadda ake matsawa kasa kamar Sin a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya a yankunanta, inda ake ta kakkaba takunkumai da bata mata suna bisa hujjar hakkin bil adama, amma aka gaza daukar matakin da ya dace kan wadanda kowa ya yi amana cewa, suna keta wannan hakki. Shin kare hakkin bil da ake yayatawa makami ne kawai na dakile kasashen dake samun ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, maimakon kare ainihin wadanda ke bukatar kariya?

A jiya Litinin, kasar Sin ta yi kira da kasashe masu ruwa da tsaki kada su kawo cikas ga batun kasancewar Palasdinu mamba a MDD, kuma kada su ci gaba da adawa da burin kasa da kasa, ganin yadda wadannan kasashe suke hawan kujerar naki kan wannan batu. Ba sau daya ba, kasashen duniya sun bayyana burinsu na ganin an samar da zaman lafiya da tabbatar da halaltattun hakkokin Palasdinawa, amma kuma wasu kasashe na yi wa wannan buri kafar ungulu. Kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka dauki nauyin gabatar da kudurin kasancewar Palasdinu cikakkiyar mamba a MDD da kuma wadanda suka kada kuri’ar amincewa da shi da sauran kudurorin da suka shafi kare hakkokin Palasdinawa da tabbatar da zaman lafiya a yankin, kamar yadda ya kamata kowace kasa dake kaunar zaman lafiya ta yi. Sai dai da alama wasu kasashe ba sa burin ganin kawo karshen wannan rikici da ma wanzuwar zaman lafiya a duniya. Kana kalaman da su kan furta na rajin kare hakkin bil adama, ya bambanta da abun da suke aiwatarwa a zahiri. Rikicin Palasdinu da Isra’ila ya kara tabbatarwa duniya wannan da kuma irin fuskoki biyu da ake nunawa a al’amuran da suka shafi kare fararen hula masu rauni. (Fa’iza Mustapha)

ADVERTISEMENT
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Maniyyatan Nijeriya

Hajjin Bana: Ranar 23 Ga Watan Mayu Za A Fara Jigilar Maniyyatan Jihar Kaduna - Hukuma

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.