Wani saurayi ya je wajen Ibrahim dan Adhama, (daya daga cikin magabata), sai ya ce masa zuciyata tana tunkuda ni zuwa sabo, ka yi min wa’azi, sai ya ce masa: Idan ta kira ka zuwa saba wa Allah to ka saba masa amma da sharuda guda biyar, sai saurayin ya ce fadi mu ji:
1. Idan za ka saba wa Allah, to ka boye a wurin da ba zai gan ka ba, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za a yi na boye masa, alhalin babu abin da yake buya gare shi, sai ya ce: yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kuma yana ganin ka?
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 3, Ta Rushe Gidaje 495 A Kano
- Yadda Hare-Haren ‘Yan Bindiga Suka Shafi Rayuwar Al’umma A Kagara – Rahoto
2. Idan za ka saba wa Allah to kar ka saba masa cikin kasarsa, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, ina zan je, alhali duka duniya tasa ce, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali kana zaune a saman kasarsa?
3. Idan za ka saba wa Allah to ka daina cin arzikinsa, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gare shi suke, sai ya ce masa yanzu ba ka jin kunya ka saba masa alhali yana ciyar da kai kuma yana shayar da kai, yana ba ka karfi.
4. Idan ka saba wa Allah, to idan mala’iku suka zo tafiya da kai wuta, ka ce ba za ka tafi ba aljanna za ka, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah ai sun fi karfina, kora ni za su yi.
5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar alkiyama ka ce: ba kai ka aikata su ba, sai saurayin ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala’iku masu kiyayewa, sai ya fashe da kuka ya tafi yana maimaita wannan kalmar ta karshe.
Don haka duk wanda zai aikata zunubi ya rika tuna wadannan abubuwan.
Allah ne mafi sani.