Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar Kano (SEMA), ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutane uku tare da raba iyalai 495 da muhallansu a Karamar Hukumar Ajingi da ke jihar.
Babban Sakataren hukumar, dakta Saleh Jili ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ajingi, yayin da yake raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa, ciki har da iyalan mutane uku da suka rasu.
- Rikicin PDP: Ba Za Mu Bai Wa Wadanda Ba Sa Kaunar Ribas Kuri’unmu Ba – Wike
- Sin Ta Kare Matakan Martani Da Ta Dauka Kan Yankin Taiwan Saboda Ziyarar Pelosi
Jili ya lissafa yankunan da lamarin ya shafa da su hada da Toranke, Kara Malama, Chuna da Balare.
Ya ce lamarin da ya faru bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranakun 3 da 4 ga watan Agusta, ya shafi mutane 495 da lamarin ya rutsa da su, ya kuma kashe uku da jikkata mutum daya.
“A madadin Gwamna Abdullahi Ganduje, mun zo nan ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da raba musu wasu kayayyaki.
“Muna fatan wannan karamcin zai kawo musu sauki tare da rage musu radadi,” in ji shi.
Kayayyakin da aka raba sun hadar da shinkafa, masara, siminti, kwanon rufi , kusa, man girki, matashin kai, wake da katifu da dai sauransu.
Jili ya shawarci mazauna yankin da su rika gyara magudanun ruwa a ko da yaushe, inda ya kuma yi kira ga wadanda ke kusa da koguna da tafkunan jihar da su bar yankin don gujewa asarar rayuka da dukiya.