Assalamu alaikum. Tambayata ita ce: shin tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya Kaurace wa matarshi ta sunnah kuma wani mataki ya dace ta dauka in har ya wuce ‘period’ din da shari’a ta halatta?
Wa alaikumus salam.
Ya halatta ya Kaurace mata tsawon watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a Suratul BaKara aya ta: 226.
Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da kansa ya ci gaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin surar ta nuna hakan.
In ya Ki komawa ya sadu da ita kuma ya Ki saki sai ta je wurin Alkali don ya ba shi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo mata ko kuma ya sake ta.
Allah ne mafi Sani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp