Wata hamshakiyar ‘yar kasuwa, mai suna Mariya Yakubu ta maka mijinta mai suna Gana Yakubu,a gaban kotu da ke Nyanya, bisa zargin sa mata magani a kan gado.
Mai karar ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai karar mijinta kotu.
- Kasar Sin Ta Mika Wasu Takardun Amincewa Da Yarjejeniyoyi Biyu Ga ILO
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
“Tun da muka gama ginin sabon gidanmu na kuma tare a cikinsa, ni da mijina muke yawan yin rikici, daga nan sai na yi yaji, Saboda matsalar yau daban ta gobe daban.
“Wani lokacin sai mai gidana zai dawo gida da wata mace. Domin ya ba ni haushi, ban taba ce masa komai ba,na yi ta daure wa,haka dai na yi ta daure wa.
“Sai wata rana, bayan na dawo gida, ina shiga dakina, sai na ga wata katuwar laya a kan gadona, sai na gaya wa mijina, sai ya nuna bai san komai ba, a kan wannan laya, sai kawai na je na gaya wa ‘yansanda. Lokacin da ‘yansandan ke bincikensa, sai ya gaya musu cewa, shi ya barbada mata magani.”
Mai karar ya roki kotu ta sa wannan mijin ya sake ta.”
A karshe, mai shari’a Shitta Abdullahi, ya dage sauraraon karar zuwa mako mai zuwa.