Assalamu alaikum, shin ko ya halatta ga matar Aure ta yi facebook, har ma da ‘charting’?
Wa alaikum assalam. Wannan tambaya ce mai wahala. Sai dai abin da zance duk abin da zai amfane ta za ta iya yi a facebook, saboda asali a shari’ar musulunci, duk abin da mutane suke aikatawa a mu’amalarsu ta yau da kullum halal ne, mutukar ba a samu wani nassi wanda ya haramta ba, ko kuma ya kasance cuta tsantsa, haka ma idan mafi rinjayansa barna ne, ka ga facebook kuwa babu wani nassi da ya haramta shi, sannan ba cuta ba ne tsantsa, tun da ana iya samun ilimin addini ta wannan kafa.
Ya kamata ta daina yin charting da wadanda da muharramanta ba in ba malamin da ta
yadda da iliminsa da tsantseninsa ba, za ta yi masa fatawa, saboda akwai maza da yawa da suke bi ta hanyar ‘charting’ don lalata matan auren da ba su da kamewa.
Wannan ya sa barin charting da mazan da ba muharramai ba, ko kuma wadanda suke neman auren matar, zai iya zama wajibi, saboda hakan yana kaiwa zuwa barna, duk abin da yake kaiwa zuwa barna, zai iya zama haramun ko makaruhi, kamar yadda malaman musulunci suka tabbatar.
Allah ne mafi sani