A yayin wani taron da aka gudanar a ranar 2 ga wata dangane da taimakawa kasashen yammacin Afirka kafa wani tsarin noman shinkafa, Wang Xuemin, mai taimakawa babban darektan kamfanin Green Agriculture West Africa wato GAWAL karkashin shugabancin kamfanin CGCOC kuma masanin ilmin noman shinkafa, ya yi karin bayani kan yawan shinkafar da ake girbewa bisa mabambantan fasahohin noma da kuma amfani da mabambantan irin shinkafa a wasu gonaki.
A shekarun baya, gwamnatin Najeriya ta bada muhimmanci kan noman shinkafa a kasar, ta kara zuba jari da taimakawa masana’antun shinkafa ta fuskar manufofi, sa’an nan ta mai da hankali kan hadin gwiwa da kasashen duniya a fannoni masu ruwa da tsaki. Dakta Olusegun Ojo, darektan kwamitin kula da irin da ake amfani da shi a aikin gona na Najeriya ya bayyana cewa, abun da ya gani a yayin taron ya burge shi sosai. Ya ce yanzu haka kasarsa ta Najeriya tana neman kara samun shinkafa ta hanyar noma mai inganci.
A nasa bangare, Shehun malami Bello Zaki Abubakar, shugaban sashen habaka harkokin kwamitin nazarin aikin gona na Najeriya, yana ganin cewa, kasashen Najeriya da Sin sun samu sakamakon da dama a fannin yin hadin gwiwar aikin gona. (Tasallah Yuan)