• English
  • Business News
Monday, August 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
1 day ago
in Labarai
0
Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Addinai da dukkanin al’adu a duniya sun yadda da aiwatar da ayyukan gaskiya, adalci da rikon amana, hasalima babu wani addinin da ya aminta da mulkin kama-karya, zalunci, cin hanci da rashawa da take hakkin bil- Adama.

Karan tsaye ga kundin tsarin mulki kasa, rashin bin umurnin kotuna, tarbarbarewar tsaro ta yadda yankuna da dama suka zama lahira kusa, gurbacewar sha’anin noma, ilmi, kiyon lafiya, tashin gwauron zabon kayan masarufi, zullumi da cin amana abubuwa ne da suka zama tamkar ruwan dare a fadin kasa.

  • Wajibi Ne Sassan Kasa Da Kasa Su Raya Ruhin Jin Kan Bil’adama
  • Wadanda Suka Mutu A Wani Hadarin Ginin Gada A Sin Sun Karu Zuwa 12

Koken jama’a kan fannin shari’a, kasa sauke nauyin hukumomin tsaro, lalacewar hanyoyin mota da suka zama tarkon mutuwa, zubewar darajar aikin gwamnati da yadda ‘yan kasuwa ke gasawa jama’a aya a tafin hannu matsaloli ne da suka yi wa jama’a katutu.

Yadda mata, matasa da dalibai suke a cikin ukuba irin ta gashin ragon layya, haka mazauna yankunan karkara ke rayuwa a saman sikelin rai- kwakwai mutu- kwakwai, kai tsaye ma za a iya cewa wasu sun yi nisa a shan maganin hawan jini, wasu kuwa rashin sanin tudun dafawa ya sa sun tsufa a makabarta.

A marra irin ta tsananin matsananciyar ukubar zubar kwalla a idon al’umma irin na kwatankwacin kukan uwar Musa, kwatsam da neman sauki a wajen ubangiji, ba zato ba tsammani a shekarar 2009 aka fara jin shirin Brekete Family wanda shine irinsa na farko kasar nan a inda jama’a ke karakainar gabatar da matsalolin da suka dabaibaye su tare da share masu hawaye.

Labarai Masu Nasaba

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

A Kudu da Arewa an shaidi gidan rediyon Brekete Family ba ya da alaka da yanki, Harshe ko addini, shirye- shiryensu suna gudana ne a tafarkin gaskiya a aikin jaridancin binciken diddigi.

Hana yaudara, zalunci da cin amana, kwato hakkokin talakawa, marasa galihu, ‘yan rabana ka wadata mu, jajircewa tare da hobbasar kwazon tabbatar da cikakken ‘yancin al’umma, kudurori ne da manufofin kashin bayan assasa Brekete Family.

Shirin Brekete Family wanda aka fara gabatarwa a tasha mai gajeren zango ta Kiss FM a Abuja shekaru 17 da suka gabata, daga baya a Crowther Lobe FM, zuwa yau ya zama alkhairi tare da kawo gyara da canza abubuwa da dama a kasar da mafi yawan ‘yan kasar ke dauke da tambarin matsala a fuskokin su.

Shirin Brekete Family shire ne na zahiri da ake gudanarwa kai tsaye ba tare da riba ba, akasin kafafen yada labarai na kasuwanci da ke samun kudin shiga. Shirin ya himmatu wajen kare ‘yancin al’umma, taimakawa wajen samun adalci ga wadanda aka cuta da karfafawa ‘yan Nijeriya taimakawa wadanda aka zalunta.

Miliyoyin al’umma ne ke sauraren shirin da suka hada da marasa karfi, manyan attajirai, ‘yan siyasa, jami’an gwamnati, sarakuna, jami’an tabbatar da doka da al’ummar wajen kasa. Shiri ne wanda al’umma ke samun mafita, daidaita sabanin fahimta ko rikicin zamantekewa haka ma shiri ne da a wasu lokutan kan yi gidauniyar tallafawa al’umma musamman mabukata da ke neman abinci da marasa lafiya.

A shekarar 2017 ce Ordinary Dakta Ahmed Isa ya assasa gidan radiyon Human Rights wanda shi kadai ne gidan radiyon ‘yancin al’umma. Haka ma gidan radiyon da TB ya bambanta da saura ta fuskar ingantattun kayan aikiin da duniyar aikin jarida a yau ke alfahari. Tun a lokacin gidan ya dauki hankalin jami’an gwamnati, al’ummar kasashen waje da ma talakawa.

A yayin da al’umma ke kasa samun mafita a hukumar kula da ‘yancin al’umma da hukumar karbar korafen- korafen al’umma na gwamnati; daga Kudu zuwa Arewa shirin Brekete Family da gidan na ‘yancin al’umma ke gabatarwa ya bayar da gagarumar gudunmuwa wajen kawar da matsalolin dubun- dubatar al’umma da inganta jin dadin su.

A shekaru da dama zuwa yau dimbin jama’a sun yi yabanya da shawarwari, nasihohi, ilmantarwa da fadakarwar da shirin ke yi a bisa ga yadda suka amfana da darussa da dama a shiraruwan da Brekete Family ke gabatarwa wadanda wasu suka yi nadamar abubuwan da suka aikata, wasu suka canza rayuwar su, wasu kuma suka yi bankwana da gurbatattun halaye.

Ba ciri ba coge dimbin al’ummar kasa sun bayyana a shekaran jiya, sun bayyana a jiya, kamar yadda suka bayyana a yau, kuma za su ci-gaba da bayyanawa a gobe da jibi yadda ubangiji ya karbii kukan su ya kawo masu Brekete Family ta hannun dan kwarai irin albarka domin share masu hawaye a mabambantan matsalolin da suka dabaibaye rayuwarsu suka hana masu walwala da ‘yanci.

Shugaban gidan radiyon, Ordinary Dakta Ahmed Isa ko Ordinary President ba ya bukatar kowace irin gabatarwa a ciki da wajen kasa a aikin da yake jagoranta na dangin da ya fi kowane dangi yawa a fadin duniya tun daga Jamhuriyar Nijar zuwa Birnin Sin.

A so shi ko a ki shi Ordinary Ahmed Isa wanda ya kwashe sama da shekaru 30 a aikin jaridanci, ya kafa muhimmin tarihin da ya yi tasiri a zukatan al’umma wanda ba za a taba iya karkare shi ba a nan kusa ko can gaba ba, a yayin da yake a raye ko bayan ya kwanta dama domin ya yi shukar alkhairin da zai yi yabanyar ayyukan alkhairi a saman mizani a wajen ubangiji a nan kusa ko can gaba.

Shirye- shiryen Brekete Family kan gudana ne a cikin kwarewa da gogewa da lakantar ciki da wajen aikin yada labarai a kololuwar mataki na kwararru da Ahmed Isa ke jagorantar hazikan kuma jajirtattun ma’aikata a dakin yada shirye-shiryen da ke Abuja da Kaduna wadanda ake kan shirin bude wasu rassan a jihohi da dama domin saukakawa al’umma kai korafi a inda suke zaune.

A shiraruwan gidan, su kan nuna damuwa da bacin rai kan yadda al’amurra da dama suka tabarbare suka fita hayyacin su a kasar nan, ta yadda wasu gurbatattun shugabanni da ma’aikata a kusan kowane bangare ke yi wa dukiyar talakawa hadiyar kafino, danne na kasa da su da gurbata aiki tare da aiwatar da abubuwan da suka ga dama a lokacin da suka ga dama tamkar a kasar da babu doka babu oda.

A kan wannan a kodayaushe kalaman Ordinary Ahmed Isa da yanayinsa kan nuna tsantsar bukatar son ganin an samu sauyi da canji mai ma’ana a kasar nan, kama daga kan fannin siyasa, aikin gwamnati, aikin hukumomin tsaro, fannin sarauta, kasuwanci, aikin gona da sauran su.

Bayanai sun tabbatar da cewar akwai dubun- dubatar korafe- korafen mabambantan al’umma daga Arewa har Kudu wadanda suka gabatar bayan cike takardun rantsuwa a kotu tare da jiran layi ya kawo kan su.

Daya daga cikin abubuwan da ke kayatar da jama’a da shirin shine yadda suke gudanar da kwakkwaran bincike ga duk wani korafi da aka gabatar kafin fara yadawa duniya ta yadda daga karshe idan an tabbatar da gaskiya, gidan kan shiga ya fita wajen kwatowa mai korafi hakkin sa daga ofishin kansila har zuwa na shugaban kasa, haka ma idan mai korafi ba ya da gaskiya kai tsaye gidan ke tozarta shi a gaban jama’a, a wasu lokutan tare da hannuntawa jami’an tsaro domin ya zama izna ga wasu. Wani abin yabawa shine yadda kai tsaye suke neman afuwar duk wanda suka yi wa kuskure ko ba daidai ba.

A sanadiyar shirin hakkin dubban al’umma ya dawo hannun su bayan cire tsammani; biliyoyin kudade sun koma hannun masu su kama daga na albashi, fansho da garatuti, kudin kwangila, kasuwanci da sauransu.. Shirin ya kuma kwato kadarori na biliyoyin kudade da suka hada da gidaje, filaye, gonaki, motoci da sauransu, haka ma hukumomin gwamnati da kamfanoni sun mayar da dimbin ma’aikata a bakin aiki bayan zaluntar su, haka ma sun jagoranci daidaita karin matsayin ma’aikata da dama. Haka ma shirin ya daidaita ma’aurata da dama da sake hada ‘ya’ya da iyaye.

Shigewa gaba da tsayuwa da Ahmed Isa ya yi wajen ganin gwamnati ta biya tsofaffin ma’aikatan rosassshen kamfanin jirgi na Nigeria Airway’s har sama da naira bilyan 40 babban abin yabawa ne da ya shiga kundin tarihi. Bugu da kari a bayyane yake gidan ba ya karbar ko kwabo ga duk wani ko wasu da suka kwatowa hakki, haka ma su kan dauki kwararan mataki ga duk wanda ya nemi ya ba su toshiyar baki.

A shiraruwan sa, a cikin hikima da kokarin karfafawa mutane da dama a kodayaushe Ordinary President kan kaskantar da kan sa, ya kan nuna bai yi karatun boko ba tare da nuna idan da ya samu damar yin karatu da ba haka ba, hasalima ya kan gabatar da shirinsa na turanci da gurbataccen turanci ta yadda idan dai za ka iya hada wannan kalma da wancan jimla za ka iya gabatar da korafi.

Sai dai a zahiri Ordinary President cikakken mai ilimi ne wanda ke da digirin – digirgir har guda biyu amma ya kan nuna ba ya da ilimin ne domin karfafawa marasa ilimi kan su dage su yi karatu ta yadda za su iya zama fiye da shi ko yin fiye da abin da yake yi. Wannan wata baiwa ce daga zababbun mutane.

Mabiya shirin Brekete Family kan ji yadda Ordinary Ahmed Isa ke fadakar da al’umma kan rike gaskiya da amana tare da nuna takaicin yadda al’umma a yau suka mayar da cin amana tamkar ado. Bugu da kari ya kan bayyana cewar ya kan kwatanta korafen- korafen da ake kawowa tamkar a gare shi ko ‘ya’yansa abin ya faru don haka yake jin zafi tare da daukar matakin gaggawa.

A bisa ga yadda ayyukansa ke tafiya da yadda girman mukami, kudi, kayan- Sarki da yawan shekaru ba su bashi tsoro, wasu suna saka alamar ayar tambayar son sanin shin wa ke daurewa Ordinary President gindi? ra’ayin wasu a kai ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi haka ma sara da sassaka… Masu saurarensa kan bayyana cewar addu”oin iyaye, malamai, dattawa, na dimbin wadanda aka zalunta da na sauran al’umma da ke yi masa fatar alkhairi ne daurin gindin sa.

An tabbatar ko da kwayar zarra Ordinary President ba ya da tsoro, ballantana fargaba, a tsaye yake kuma a jajirce tare da daukar kowane irin kwaram da kwaramniya, ya tsani cuta ballantana zalunci, an shaide shi da alhairi da ayyukan alhairi ta hanyar zama bango majinginar bayin Allah tare da mutunta kowa a kan matsayin sa.

Ba sai an fada ba Brekete Family na fuskantar kalubale sosai musamman daga gwamnati a matakai daban- daban da al’umma wadanda ke ganin shirin na bankado rashin gaskiyar su da sa su aikin dole da ba su yi niyya ba tare da bin ka’idojijn da a baya suke takewa, suna ganin shirin a matsayin barazana ta yadda a fili yake fallasa kasawar su tare da kira gare su da idan za a gyara a gyara.

Baya ga zagon kasa daban- daban da wasu hukumomin gwamnati da ‘yan siyasa ke yi wa Brekete Family haka ma marasa gaskiya da dama da shirin ya kwato hakkin wadanda suka zalunta kan gurfanar da Ahmed Isa a kotu ta yadda akwai daruruwan karar da aka shigar da gidan radiyon da jagoransa a kotuna daban- daban. A kan wannan Ahmad Isa ya bayyana cewar suna da kwararrun lauyoyi sama da 400 da ke kariyar su a mabambantan shariu wadanda kuma suke tsayawa jama’ar da aka zalunta kyauta a kotuna.

A shirye- shiryensa Ahmed Isa yana matukar nuna tsantsar tsabar kishin Arewa tare da kuka da kokawa kan yadda Arewa take a tutar baya da son ganin al’amurra sun daidaita har Arewa ta samu ci-gaba mai amfani da dorewa tare da gogayya da ‘yan uwanta da ke Kudancin Kasa.

Hasalima a kan kishin Arewa da son daukakarta ne dalilin da yasa kafar yada labaran ta ‘yancin al’umma ta dauki ciki tare da haihuwar Brekete Family Arewa, shirin musamman da aka assasa domin amfanin al’ummar Arewa wadanda kan gabatar da korafin su a cikin yarukan Arewa, galibi a cikin harshen Hausa.

Addu’o da fatar alhairin da jama’a ke yi wa Brekete Family, Ahmed Isa da ma’aikatan su bakidaya ya nuna irin karfin gidan da girman matsalolin al’umma da suke kawarwa. Daukar nauyin aikin marasa lafiya, tallafin jari, tallafin karatu, tallafin gina, samarwa mutane aiki, da koya masu sana’o’i domin su zamo masu dogaro da kai abubuwa ne da Ahmed Isa ke yi da zuciya daya domin neman yardar Allah.

A yayin da attajirai musamman wadanda suka yi fice wajen taimakawa al’umma ke izza da alfahari da nuna isa, a bangarensa Ahmed Isa ya nesanta kansa da wannan domin mutum ne maras girman kai, mai dattako da sanin ya kamata.

A shiraruwan sa ya kan bayyana irin wahala da ukubar da ya sha a rayuwa, irin sana’o’i na wahala da ya gudanar da yadda ko kadan ba ya son ganin yamma ta yi domin ba ya da inda zai kwanta da dare. A kalamansa ya kan ce “Allah ne ke yin amfani da ni wajen taimaka maku amma ni ba kowan kowa ba ne kuma ban fi ku da komai ba.”

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, shugaban Malaman Birnin Tarayya, Abuja wanda ke bayar da gudunmuwa a shirin ya bayyana cewar korafe- korafen da jama’a ke kawowa a gidan wadanda ba a yadawa duniya sun zarce wadanda jama’a ke ji a kullum.

Malamin wanda kuma shine wakilin Malaman Bauchi ya bayyana cewar a cikin kashi 100 na korafe- korafen da jama’a, wadanda a ke gabatarwa a radiyo ba su fi kashi 20 ba wadanda a cikin maslaha a ke zama a cimma matsayar sasantawa.

A cewarsa akwai abubuwa masu tashin hankali, ban haushi da ban tsoro wadanda har jama’a ke tambayar wai anya kuwa a cikin al’umma ake gudanar da wadannan abubuwan?” a cewar Sheikh Duguri wanda ya bayyana hakan a shirin Brekete Family Arewa a ranar Litinin din makon nan a yayin sauraren korafin wata matar aure A’isha wadda mijin ta ke dukan ta, hana ta abinci, saduwa da ita a yayin azumi da saduwa da ita a yayin jinin al’ada.

Zuwan Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo a gidan radiyon a 2019 ya sa al’umma kara sallamawa Brekete Family domin ya kafa tarihin zama gidan radiyo na farko da ke yada shirin zahiri da ya karbi bakuncin mutum mafi daraja ta biyu a kasa wanda hakan kadai ya tabbatar da cewar Ordinary Ahmed Isa ba kyalle ba ne babban bargo ne.

Shakka babu da za a samu ire- iren Brekete Family ko Ordinary President a kasar nan a mabambantan wurare da za su yaki zalunci, tabbatar da ‘yancin al’umma, share hawayen su da samar masu kyakkyawar makoma da al’umma sun yi bankwana da dimbin matsalolin da suka yi masu tarnaki suka hana masu ci-gaba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Brekete
ShareTweetSendShare
Previous Post

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

Next Post

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

Related

Labarai

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

1 hour ago
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

2 hours ago
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC
Labarai

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

5 hours ago
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya
Ra'ayi Riga

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

7 hours ago
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas
Labarai

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

10 hours ago
An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa
Labarai

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3, Sun Kwato AK-47 A Kebbi

11 hours ago
Next Post
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

LABARAI MASU NASABA

Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto

August 24, 2025
Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

Ƴansanda Sun Kama Wani Gawutaccen Ɗan Fashi Da Garkuwa Da Mutane A Nasarawa

August 24, 2025
Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

Za A Bude Cibiyar Watsa Labarai Game Da Bukukuwan Nasarar Yaki Da Harin Japan 

August 24, 2025
An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

An Kaddamar Da Makon Fina-finai Da Shirye-shiryen Talabijin Na SCO A Qingdao

August 24, 2025
CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

CMG Za Ta Gabatar Da Bikin Faretin Soja Na Beijing Cikin Harsuna 85 Ga Duk Fadin Duniya 

August 24, 2025
Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

Akwai Katin Zaɓe Fiye Da Dubu 367 Da Ba A Karɓa Ba A Kano – INEC

August 24, 2025
An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

An Kaddamar Da Gini Mara Fitar Da Hayakin Carbon Irinsa Na Farko A Duniya

August 24, 2025
Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

Kasar Sin Ta Gudanar Da Bita Na 3 Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasara A Yakin Kin Harin Japan

August 24, 2025
Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

Ya Kamata A Kiyaye Sahihin Tarihi Da Rike Gaskiya

August 24, 2025
Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

Tanko Yakasai Ya Nuna Takaici Kan Rashin Samar Da Kamfanin Sarrafa Fata A Kano Kamar Na Legas

August 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.