An gudanar da wani shirin ba da horo na kasa da kasa tsakanin Sin da Senegal kan cikakken tsarin masana’antar gyada a birnin Qingdao na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin.
Wanda aka kaddamar a ranar 6 ga watan Yuli, shirin na kwanaki 15 ya tattaro mahalarta 14 daga kasar Senegal, wadanda suka kunshi masu bincike, da jami’an gwamnati da kuma ‘yan kasuwa.
- Sin Ta Gina Tsarin Layin Dogo Da Manyan Hanyoyin Mota Da Na Aikewa Da Kunshin Sakwanni Mafi Girma A Duniya
- Kamfanonin Kera Kayan Likitanci Na Duniya: Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Kasar Sin Babban Ginshiki Ne
Kwas din ya mayar da hankali ne kan koyar da kwarewar kasar Sin a fannin noman gyada, ciki har da dabarun tsimin ruwa, da yaki da kwari da cututtuka da kuma iya kula da filayen noma.
Darektan Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Senegal (ISRA) Ibrahima Sarr, ya ce, “Wannan kwas na horarwa ya kayatar da mu matuka, wanda ya kara mana kwarin gwiwa wajen inganta tsarin masana’antar gyada a Senegal.”
Sarr ya kara da cewa, “Ta hanyar inganta sauye-sauye da daga darajar tsarin masana’antar gyada, kasar Senegal za ta iya bunkasa masana’antar gyadarta ta cikin gida, da habaka kasuwanci ta shafin intanet da sauran fannoni, ta yadda za a samar da karin guraben ayyukan yi.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp