Gidauniyar Tattara Harajin Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFund) ta nemi a kara yawan harajin da ake karbar don tallafa wa harkar ilimin manyan makarantu zuwa kashi 3 a cikin dari. Gidauniya ta bayyana cewa, neman karin ya zama dole ne don a samu kudaden bunkasa harkar karatun manyan makarantun kasar nan yadda yakamata.
Shugabanin hukumar sun bayyana cewa, ana fuskantar matsaloli wajen cimma manufar kafar gidauniyar saboda yadda ake fuskantar matsalar tattalin arziki ba wai a Nijeriya kadai ba har ma a sauran Kasashen Afrika, inda gwamnatoci ke fafutukar farfado da hanyoyin tattara haraji ga shi kuma suna fuskantar basussukan cikin gida dana kasashen waje, kara wani haraji zai kai haifar da matsalolin ne da ba a sai iyakarsu ba.
Yakamata a lura da cewa, gwamnatin tarayya ta kafa hukumar TETFund a shekarar 2021 ne ta zama wata kafar bayar da tallafi ga manyan makarantun kasar nan musamman ma abin da ya shafi gine-gine da samar da kayyakin aiki ga manyan makarantun a fadin tarayyar Nijeriya.
An dora harajin tallafin ilimin ne ga kanfanonin Nijeriya inda suke bayar da kashi 2.5 na ribar da suka samu a duk shekara don taimakawa sashen ilimin manyan makarantun Nijeriya.
Yana kuma da muhimmanci a sani cewa a tsakanin shekarar 1998 zuwa 2018, TEDFUND ta rarraba wa manyan makarantun kasar nan fiye da naira Tiriliyan 1, manyan makarantun sun hada da jami’o’i, Makarantar Fasaha da makarantun Kwalejojin Horar da mayan malamai, ya zuwa shekarar 2021, jimillar manyan makarantu 221 suka amfana daga tallafi daban-daban na TEDFUND sun kuma hada da Jami’o’i 87, Makarantar Fasaha 65 da makarantun Kwalejojin Horar da mayan malamai 69. Wannan namijin kokarin ne ya sa hukumar ke neman a karin harajin da take karba don karin manyan makarantu su amfana da wannan tallafin, suna neman a kara harajin akkalla zuwa kashi 0.5.
Ra’ayin wannan jaridar a nan shi ne lallai lamarin ya zama dole in aka lura da yawan yaje-yajen aikin da malaman manyan makarantu ke yi da kuma halin tabarbarewar da makarantunmu ke ciki da kuma babbar matsalar wadda take ci wa manyan makarantun tuwo a kwarya, su ne na kudaden gudanarwa da ya yi matukar karanci.
A ra’ayinmu abin takaicin shi ne yadda lamarin samar wa manyan makarantu kudaden gudanar da ayyukansu ya zama tashin hankali, wannan kuma tun daga gwamnatocin da suka gabata ne, wasu masana sun bayyana cewa, Nijeriya na bukatar akalla Naira Tiriliyan 2 don farfado da sashin ya yi daidai da takwarorinsa na kasashen duniya.
Rahoto ya nuna cewa, a tsakanin shekara 6 (2016 zuwa 2021) Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta samarwa bangaren ilimi Naira Tiriliyan 55.3, amma Naira Tiriliyan 3.5 kasa da kashi 10 kena suka samu shiga hannun bangaren.
Tabbas wannan abin takaici ne matuka, kuma bai kamata ba, hakan kuma na daga cikin korafe-korafen kungiyar Malamai ta ASUU wanda ya kai su ga shiga yajin aiki har na wata 16 tun da aka shiga tsarin mulkin dimokradiyya a kasar nan a shekarar 1999, babbar korafinsu yana tattare da batun samarwa da jami’o’in kudaden gudanarwa ne.
Masana sun bayyana cewa, gwamnatin tarayya kadai ba za ta iya samarwa manyan makarantun kudaden da suke bukata ba musamman ma ganin yadda ake fuskantar karancin kudaden shiga da kuma yadda ake fuskantar karuwar manyan makaranhtu ba tare da wani tsari ba, ana yi ne saboda biyan wasu bukatu na siyasa.
Babu tantama cewa, TETfund ta yi gaggarumin kokari wajen samarwa wasu manyan makarantu kayan aiki da gine-gine masu inganci, amma lalle akwai karin bukatar aiki sosai a bangaren. Tabbas yawancin manyan makarantunmu na fuskantar lalacewar gine-gine kamar dakunan kwanan dalibai da wuraren karatu dama hanyoyin cikin jami’o’in duki sun lalace, wasu wuraren ma ba zai yiyu a ce dandama na zama a wurin ba. Wannan ya sa ya zama dole a samar wa da manyan makarantunmu isasssun kudade ta yadda za su yi gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya da suka cigaba.
Amma a halin yanzu ‘yan Nijeriya da dama suna nuna damuwarsu a kan yadda kananan da matsakaitun kamfanoni suke fuskantar haraji daban-daban, a wasu jihohin kamfanoni na biyan haraji daban-daban har fiye da kashi 20. Hukumar kula da tattara haraji ta bayyana cewa, a Nijeriya mutane 10,006,304 ke biyan haraji wanda ke nuna kashi 5 kenan nan ke daukar nauyin al’ummar Nijeriya da suka kai fiye da mutum miliyan 200.
A ra’ayinmu yakamata ba fadada kokakrin karbar harajin ya hada da karin mutane don kaucewa dora nauyi a kan wasu ba’adin mutane kadan, ya kuma kamata a kaucewa karbar haraji barkatai a hannun mutane.
Muna goyon bayan karin akalla kashi 3 na harajin ilimi saboda mun yi imanin hakan zai matukar taimakawa wajen maganin matsalolin da bangaren ilimin manyan makarantun Nijeriya suke fuskanta. Ya kuma kamata manyan makaratunn kasar nan su samarwa kansu salon samun kudaden shiga kamar dai yadda ake samu a kasashen Turai da Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp