• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Gaskiya Ta Bayyana Kan Bullar Mata Masu Shan Jini

Mun wallafa a ranar 8 ga Satumba, 2023

by Rabi'u Ali Indabawa and Abdullahi Muh'd Sheka
1 year ago
in Rahotonni
0
Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Gaskiya Ta Bayyana Kan Bullar Mata Masu Shan Jini
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Tun daga karshen watan Agusta aka rika yada jita-jitar bayyanar wasu mata da suke shiga gidajen mutane wadanda ake musu lakabi da ‘masu shan jini’ a wasu sassa na Arewa musamman Jihar Kano.

An ce wadannan mutane suna yawo ne gida-gida a lokacin da ska tabbatar da mazaje ba sa gida, inda da zarar sun shiga, abin da suke fara nema shi ne a taimaka musu da ruwan sha ko wani abu, wanda kuma da an taimaka musu da abin da suka bukata, to wacce ta ba da taimakon sai a ga ta yanke jiki ta fadi, daga nan lamarin ya kai ga ta rasa ranta.

  • Harin Filato: Gwamnati Ba Za Ta Huta Ba Har Sai An Hukunta Maharan – Shettima 
  • Yadda Aka Shirya Wa ACG James Sunday Bikin Taya Murnar Karin Girma A Gombe

Masu yada maganganun sun ce irin wannan ibtila’i ya faru a unguwanni daban-daban a cikin Birnin Kano.

A wasu bidiyo da suke yawo a kafofin sadarwa na zamani ana ganin yadda ake dukan wadannan mata yayin da aka kama su, sannan kuma a lokacin da ake yi musu tambayoyi sukan kasa ba da wata gamsasshiyar amsa da za ta fahimtar da mutane yadda gaskiyar lamarin yake.

An samu irin wannan lamarin a unguwannin Hotoro, Zango, Rijiyar Lemo, Gwagwarwa, Kwana Hudu Medile, da sauran wasu unguwanni da ke cikin birnin Kano.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro

Baya ga haka, akwai wani bidiyo da yake yawo na wasu mata ‘yan kauye da aka nuna wasu matasa na yi musu tambayoyi, amma su kuma maganarsu ba irin ta ‘yan Jihar Kano ba ce mutanen Sakkwato ne.

Sannan akwai wani bidiyo na wata baiwar Allah da lamarin ya shafi ‘yarta wacce ‘yar ba ta kai shekara guda da haihuwa ba, inda uwar take bayanin yadda ta rasa ‘yarta ta irin wannan hanya.

Kamar yadda LEADERSHIP Hausa ta bi diddigi, tun da farko daga yankin Kankara da ke Jihar Katsina aka fara samun bullar irin wannan labari, inda aka ce wata tsohuwa ta shiga wani gida inda ta bukaci a taimaka mata da ruwa ta shiga ban daki, shigarta ke da wuya sai matar gidan ta fadi. A cewar labarin sai jini ya fara kwarara daga jikin matar, daga nan sai ita bakuwar ta kama hanyar ficewa daga gidan a kan hanyar fita suka ci karo da mijin matar, tun da bai san abin da ke faruwa ba sai ya bar ta  ta wuce, yana shiga gida sai ya tarar da matarsa cikin jini, hakan tasa ya dawo da gudu, ya nemi gudunmawar al’umma aka kama matar. Bayan yi mata tambayoyi sai ta bayyana cewa su 100 aka turo Jihar Katsina, yanzu haka an kashe tara daga cikinsu, ita ce ta goma. In ji majiyarmu.

Sakamakon yadda lamarin ya yi kamari a tsakanin al’umma, LEADERSHIP Hausa ta gudanar da Shirin Tattaunawa ta Manhajar Twitter Space, inda ta gayyato mai magana da yawun ‘yansanda, reshen Jihar Kano, SP Haruna Abdullahi Kiyawa da kwararriyar mai horarwa da warware mishkilar zamantakewa, shugabar Cibiyar Nurul Huda, Hajiya Fatima Bamalli domin warware zare da abawa kan wannan al’amari.

A jawabin da ya yi, SP Haruna ya tabbatar da wannan jita-jita da ake yadawa inda ya ce tuni rundunarsu ta kaddamar da bincike, yana mai cewa, “Mun samu rahotanni 14 cikin kwana 5 na rufar wa mata da zargin ‘yan shan jini ne, kamar a unguwar Hotoro an samu guda uku, Zango 4,” in ji shi.

“Duk mun gudanar da bincike daya bayan daya, duk binciken da muka yi ba mu samu ko daya a cikin matan da ake zargi da laifin shan jini ba, abu ne na Allah wadai. A Unguwar Kwana 4, wasu ‘yan mata ne suka kai caji a wani gida, kawai daya ta ce wa matar gidan za ta je bandaki sai matar ta kwarma ihu wai budurwar ‘yar shan jini ce, shi kuma maigida da ya zo maimakon ya yi amfani da hankali kawai sai ya kulle ‘yan matan a daki,’yan unguwa suka taru, matar gidan ta daki wadda take zargin, ‘yansanda ne suka kubutar da su.

A nata bangaren, Shugabar Cibiyar Horarwa ta Nurul Huda, Hajiya Fatima Bamalli Bamalli ta yi bayanin cewa,

“Ana ta yadawa muna ganin bidiyos, ana ce wa mutane a daina ba da taimakon ruwan sha kuma a daina bude kofar gida. Gaskiya kowane Dan’adam akwai yakininsa. Da aka fara yadawa, na ce wannan tsafi ne amma ni ban yarda da shi ba. Na daya dai, mu mata daga mahangar addini, Allah ya umarci Manzon Allah ya fada wa muminai a killace mata a gida. Kuma haka nan mata a yanzu ana business ana aiki amma ya kamata a yi bisa sharuddan addini. Abin da ya sa abin ya fi faruwa da mata saboda mu ne muke da sakaci, Wasu make-up da ake yi mara ma’ana, to mai yin irin wannan ne ma abin zai iya kamata. Sannan an manta da yin azkar da addu’o’i shi ya sa ma idan an yi abin zai kama mutum.

“Ni dai ban yarda da abin ba dama. Ba na jin akwai wanda zai zo ya ce na ba shi ruwa na hana shi. Idan ka ciyar ko ka shayar Allah zai ba ka lada. To don me za a hana mutane yi? Ni da nake son yin taimakon saboda Allah ba na tunanin wani abu zai faru in ba alheri ba. Ya kamata mu koma wa wayewar addinin musulunci ba na bature ba kawai. Idan kuma kina azkar wani abu ya faru to ka sani wannan jarrabawa ce kawai. Kuma Allah na iya sa haka ta zama kaffara.” In ji ta.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Rawar Da Kasar Sin Ta Taka A Duniya

Next Post

Xi Jinping Ya Yi Jawabi A Taron Sabuwar Shekara Ta 2024 Na Majalisar CPPCC

Related

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi
Rahotonni

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

4 weeks ago
Janar Tiani Ya Fara Sabon Mulkin Shekaru Biyar A Nijar
Rahotonni

Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro

1 month ago
An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya
Rahotonni

An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Tsakanin Manoma Da Makiyaya

1 month ago
Donald Trump Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Tuhumar Da Ake Masa
Rahotonni

Amurka Ta Sayi Kayayyakin Nijeriya Na Dala Miliyan 643 A Wata 2 – Rahoto

1 month ago
Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi
Rahotonni

Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi

1 month ago
Tinubu
Manyan Labarai

Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027

2 months ago
Next Post
Xi Jinping Ya Yi Jawabi A Taron Sabuwar Shekara Ta 2024 Na Majalisar CPPCC

Xi Jinping Ya Yi Jawabi A Taron Sabuwar Shekara Ta 2024 Na Majalisar CPPCC

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

May 16, 2025
Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

May 15, 2025
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

May 15, 2025
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

May 15, 2025
Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya

Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025

May 15, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Yi Karin Haske Kan Huldar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

May 15, 2025
An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe

May 15, 2025
HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

HOTO: Ofishin Tsohon Shugaban Kasa Shagari Bayan Shekara 42

May 15, 2025
Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

Shawarwarin Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka Sun Haifar Da Managarcin Sakamako

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.