Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun yaba wa kokarin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wajen inganta bangaren duba da gagarumar nasarar da ake samu biyo bayan ayyana dokar ta baci da ya yi a fannin ilimin jihar.
Sun bayyana hakan ne cikin shirin tattaunawa da LEADERSHIP ta shirya a shafinta na X da akafi sani da twitter inda masu ruwa da tsakin suka yaba da da matakan da gwamnatin ke dauka.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Birnin Baoji Na Lardin Shaanxi Da Birnin Tianshui Na Lardin Gansu
Cikin jawabinta, babbar hadimar Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan ilimin Mata Hajiya Yesmin Mukhtar, ta ce gwamnan ya gyara makarantu da dama da ke cikin halin kaka-ni-ka-yi tare da bude wasu da a da can baya an nuna musu halin ko in kula.
Sauran ci gaban da aka samu kamar yadda sauran masu tofa albarkacin bakinsu irin su tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Farfesa Usman Moddibo da mai mallakar shafin Arewa Twitter, Malam Abdullahi Nasarawa suka bayyana, akwai kaddamar da manyan ayyuka na gyaran makarantu da kuma inganta kwazazon malamai.
Duk sun yaba wa gwamnatin jihar kan wasu daga cikin jiga-jigan kokarinta na inganta harkar ilimin irin su ware kaso 29 na kasafin jihar ga bangaren ilimi da diban malamai fiye da 5,600 da biyan kudaden jarrabawar WAEC da NECO ga dalibai da bude cibiyoyin samun ilimin zamani na na’ura mai kwakwalwa.
Sai dai sun ce duk da haka akwai sauran aiki a gaba wanda idan aka mayar da hankali tabbas za a yi nasarar har karshe.
Shi ma kwamishinan ilimi na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana bukatar yaba kokarin da gwamnatin ke yi ta hanyar ba ta duk wani hadin kai da take bukata don samun nasara.
Zuwa yanzu dai, daga cikin gagarumin kokarin da take yi, Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fitar da fiye da Naira Biliyan 2.7 domin gina ajujuwa 176 da ofisoshi 88 a sassan kananan hukumomin jihar 44.