Hukumar yaki da fatara da kirkiro da ayyuka a jihar Adamawa (PAWECA), ta shirya kawar da fatara da talauci tsakanin al’ummar jihar kafin shekarar 2027.
Hajiya A’isha Bawa, shugabar hukumar ce ta bayyana haka a Yola, inda ta ce, hukumar ta kashe fiye da Naira biliyan 4 da miliyan dari hudu (4.4 billion), wajen tallafawa matasa maza da mata don samun abin dogaro da kai, daga 2019 zuwa yau (2024).
- Rana Ba Ta Karya: Habakar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Ba Mahassada Kunya
- Gwamna Dauda Ya Sanar Da Ɗaukar Ma’aikata Da Samar Da Garejin Tireloli A Zamfara
Ta ci gaba da cewa “PAWECA ta cimma nasarori da dama, a fannin tallafawa talakawa da marasa galihu, tun bayan farfado da hukumar a 2019 bisa kudurin gwamna Ahmadu Fintiri na samar da ingantacciyar gwamnati da kyautata rayuwar jama’a.
“Wadanda su ke cin gajiyar shirin a halin yanzu su na amsar naira dubu 10, a kowani wata, akwai masu dubu 15, da 20, da dubu 30, da masu amsar dubu 50, ya danganta da a wani fanni mutum yake, duk da cewa, Gwamnatin da ta gabata, dubu 5 ta ke biya.
“Hanyar da muka dauka, da yardar Allah kafin shekarar 2027, mun kuduri aniyar kawar da talauci da rage radadin fatara a tsakanin al’ummun Adamawa.” Inji Bawa.
Hajiya Aisha, ta kuma bayyana shirin bude cibiyoyin koyar da sana’o’in dogaro da kai 10, da ke bangarorin jihar don bunkasa sana’o’in dogaro da kai a fadin jihar.
“PAWECA za ta farfado da kanana da matsakaitan masana’antu, yanzu haka, mun yi wa kananan masana’antu hannu fiye da 7,000 Rijista, kuma da yawansu mun ba su tallafi don bunkasa sana’o’insu.
“Mun tanadi kyawawan tsare-tsare ga marasa karfi da marasa galihu, mun kuduri aniyar ganin da yardar Allah, nan da shekarar 2027, za mu cimma nasarar kawar da talauci, fatara da rashin sana’a a Adamawa” in ji Aisha Bawa.