Kwanan baya, kasar Sin ta gabatar da takardar farko ta bana, wadda ta kasance a matsayin sanarwar farko ta manufofin gwamnati da mahukuntan tsakiya na kasar Sin suke fitarwa a farkon kowace shekara, wadda ake daukarta a matsayin manunin muhimman manufofin da gwamnati za ta fi bai wa fifiko. Inda a karo na farko, takardar ta gabatar da manufar “raya sabon ginshikin bunkasa ayyukan gona”, da zummar tattara abubuwa na zamani dake shafar samar da kayayyaki. Alkaluman da hukumar aikin noma da raya karkara ta Sin ta samar sun shaida cewa, yawan gudunmawar da ci gaban kimiyya da fasaha a bangaren aikin noma ta bayar ya kai kashi 63.2% a shekarar 2024.
Alal hakika, bunkasar aikin noma a bangaren kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ya fidda wata sabuwar hanya ta hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin zamanantar da aikin gona. A halin yanzu, shinkafa da ake tagwaitawa mai fasahar Sin ta samu karbuwa a kasashen Afirka fiye da 20, matakin da ya taimakawa wadannan kasashe wajen daga yawan shinkafa da suke samu daga ton 2 a ko wace hekta zuwa 7.5. Ya zuwa karshen shekarar 2023, Sin ta kafa cibiyoyin ba da misali kan kimiyyar aikin noma 24 a kasashen Afirka, inda ake kokarin yayata fasahar shuka masara mai matukar armashi da fasahar shuka kayayyakin lambu da hayayyafar rogo mai saurin nuna da dai sauran fasahohi na zamani fiye da 300, kana manoma fiye da miliyan 1 suna cin gajiyarsu, wadanda suka yi matukar tallafa wa aikin zamanantar da aikin gona a nahiyar.
Hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren zamanantar da aikin gona hakikanin mataki ne da Sin ta dauka na gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga dukkan al’umma a bangaren aikin noma, wanda ya taimakawa kasashen Afirka wajen samun isasshen hatsi na dogaro da kansu ta amfani da karfin kirkire-kirkire a bangaren aikin gona. Kuma ta zama abin koyi na kulla sabon salon huldar kasa da kasa na hadin gwiwar cin moriyar juna da samun bunkasa tare. (Mai zane da rubutu : MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp