• English
  • Business News
Sunday, July 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah

by Rabi'at Sidi Bala
4 months ago
in Taskira
0
‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

TASkIRA shafi ne daya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi bikin sallah me gabatowa, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; “Wane tanadi aka yi wa sallar bana?, A kowace shekara tsakanin mata da maza akan fidda wani yayi/anko, shin a wannan sallar ma an yi irin wannan tanadin?, Wane irin kaya ake sha’awar sakawa ranar sallah?, wane irin abinci da abin sha ake sha’awar ci bayan sakkowa daga sallar idi?, ina da ina ake son zuwa ranar sallah?”.

  Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Amina Abdul’aziz Jihar Bauchi:

Eh! tabbas akwai anko tsakanin mata na hijab, wanda ya shigo na yayi, shi yadin hijab din ana masa yanka iri daya ne ako’ina, sai dai bambance-bambancen kala kawai. Gaakiya ni dai a nawa  tsarin ina sha’awar saka Atamfata doguwa, da kuma hijab din da za ai yayi in za a tafi idi, in andawo kuma sai in sa mayafin da zai shiga da atamfar. Abincin da na ke sha’awar ci bayan saukowa daga sallar idi akwai; Wainar shinkafa, fried rice da kuma lemo mai sanyi na sovo. Ina son zuwa gurare da dama ranar idi kamar gidan kawayena mu hadu, zuwa wajen shakatawa da dai sauransu.

Labarai Masu Nasaba

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

Sunana Naja’atu Baffa Jihar kaduna:

Ni dai a gaskia ban son akwai wani anko da za ai wannan sallar ko babu ba. Ina son saka takalmi mai dan tudu ba sosai ba, sai mayafi blue black, sai atamfa ta riga (half bubu) da ‘skirt’, sai sarka da dankunne da Awarwaro ‘silver’. Ina sha’awar cin Snacks irinsu meatpie, samosa, doughnut da kuma cake, sai kuma Yoghurt mai inibi. Ina son in ziyarci kanwar babata wacce take a cikin garin Adamawa.

Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To batun shidimar sallah sai mu ce Alhamdullilah domin duk tanadin da mutum yayi sai ya kare, duba da yadda kayayyakin suturu ko tufafi suke tsada don haka sai mutum yayi amfani da abun da ya samu, domin gudanar da bikin sallar cikin kwanciyar hankali ya fi komai dadi. To magana ta gaskiya shadda ita ce kalar kayan da zai fi yawa domin ita shadda ba a daina yayinta kuma tana daga cikin kalar suturar da duk mai hali ko sukuni zai so ya dinka, amma wasu kuma za su dinka yaduka domin kowa da irin kalar suturar da ta fi burge shi. To ni dai nafi sha’awar farin kaya musamman yadda manyan kaya ma’ana riga, binjima da wando da kuma hula fara wannan sune kalar suturar dana fi so musamman lokacin zuwa idi. Batun babu zabi duk wanda na samu zan ci, amma nafi son biskin alkama da miyar yakuwa ko jar miya. To da farko dai Masallacin idi shi ne guri na farko, sannan kuma sai ziyarce-ziyarce gidajen ‘Yan’uwa da abokan arziki.

Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar kaduna:

An yi wa sallah tanadi da dama kamar kayan da za a sa, Lalle, kitso, da sauransu. Bana tunanin gaskiya akwai wani anko da aka fitar domin a halin yanzu ko wa abin da Allah ya hore mai zai saka. Ina son saka shadda mai ‘stones’, ina son cin funkaso, tuwon shinkafa da miyar Agushi wadda ta ji ganda, kaji da kayan ciki, sai lemon ginger, sai farfesun zallar naman zabi.

Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:

Ana yin tanadi wa bukukuwan Sallah da yawa, amma dai ni kam babu tanadin dana yi wa sallar bana, batun anko  ko yayin kayan da ake siya, ni dai kam har yau ban lura ba, amma dai bana Iyalai na suna sha’awar Shadda, kuma gaskiya ba na ina sha’awar cin sakwara da hadadden lemu (Ubangiji Allah ka kara hore mana). A bisa al’ada kuma muna kaiwa ‘yan’uwa da abokan arzuka ziyara, tare da taya murnar kammala ibada. Ubangiji Allah karva mana ibada, ya sa mun dace.

Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Tanadin dana yi wa wannan sallah shi ne ina so ta same ni cikin koshin lafiya da kuma ‘yan canji a cikin aljihuna. Wannan shekarar ta zo da son yin wankan shadda wato shampoo ita ce kowacce saurayi ko budurwa take/yake son sakawa duk da tsadar rayuwa da muke fama da ita. Ina sha’awar saka farar sutura ko shadda da farar hula a lokacin tafiya sallar idi. Abincin da nake muradin ci sh ine funkaso da jar Miya da naman kaji. Ina son kai ziyara zuwa gidan ‘Yan’uwa da abokan arziki in sha Allah.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar kano Rano LGA:

Babban tanadi shi ne Allah ya nuna mana ita muna raye da koshin lafiya. Haka ne kam duk da ana cikin yanayi ba za a rasa wadanda suka yin ba amma mu masu iyali iya yaranmu da iyayensu muka samu muka yi wa. da son samune ni dai sabuwar shadda fara idan kuwa ba ita ba to na sami koda koriya ce ko yadi shi ma fari ko koren. Waina da kunun daka ko na alkama da miya. Bayan dawowa daga sallar idi zan je gidan mahaifina da kuma gidan surukaina sai kuma na ‘yan’uwa da abokaina na kusa domin kara sada zumunci. Allah ya karvi ibadunmu.

Sunana Aisha T. Bello Jihar kaduna:

Sallah bikin daya rana in ji masu magana, a gaskiya na yi ma wannan sallah tanadi babba in Allah ya sa muna da rabon gani. Zan sanyaya raina ta samar da abun da na fi so a ci da sha, zan kai ziyara, zan je kallon hawan sallah, sannan zan kikkira ‘yan’uwa domin taya su barka da sallah da yardar Allah. A gaskiya bana jin wannan sallar akwai wani tanadi na anko kamar kullum, duba da yanayin rayuwa ana ta abun ci da sha ne, ina sha’awar saka doguwar riga da salla in sha Allah, sannan in sa babban mayafi in halarci sallar idi. In Allah ya ba ni dama ina so in kai ziyara jihar katsina don ganin dangina da ‘yan’uwa in sha Allah.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Sallah ƘaramaTaskira
ShareTweetSendShare
Previous Post

Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi

Next Post

An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya

Related

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri
Taskira

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

8 hours ago
Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
Taskira

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

4 months ago
Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?
Taskira

Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?

5 months ago
Maganin Zubewar Mama Da Yadda Ake Gyara Shi 
Taskira

Yadda Mata Ke Daukar Yara Don Taya Su Aikin Gida

7 months ago
Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?
Taskira

Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?

10 months ago
Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?
Taskira

Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?

1 year ago
Next Post
An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya

An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi

Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi

July 20, 2025
Yanzu Haka Muna Bincikar Gwamnoni 18 – Shugaban EFCC

Yanzu Haka Muna Bincikar Gwamnoni 18 – Shugaban EFCC

July 20, 2025
Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji

Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji

July 20, 2025
Ki Bar Auna Yadda Mijinki Yake Miki Da Yadda Wani Yake Wa Matarsa

Ki Bar Auna Yadda Mijinki Yake Miki Da Yadda Wani Yake Wa Matarsa

July 20, 2025
Ko Kin San… Yadda Ake Magance Cutar Sanyi Ga Ma’aurata (Infection)

Ko Kin San… Yadda Ake Magance Cutar Sanyi Ga Ma’aurata (Infection)

July 20, 2025
Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

July 20, 2025
Amfanin Kabewa A Jikin Mace

Amfanin Kabewa A Jikin Mace

July 20, 2025
Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

July 20, 2025
Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

July 19, 2025
An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

July 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.