A yayin da ‘yan Nijeriya ke tsumayar zuwan ranar 29 ga watan Mayu, ranar da za a rantsar da zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu, tuni shirye-shirye suka yi nisa na saukar mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da mika ragama ga sabuwar gwamnati.
Daga abubuwan da ke gudana a Abuja na shirin saukar Shugaba Buhari, akwai batun sauyin muhalli. Dama an saba, duk lokacin da za a yi canjin gwamnati, manyan muhimman ‘yan siyasan kasar nan musamman wadanda ke zaune a gidajen gwamnati kan tattara nau-i-nasu zuwa inda za su ci gaba da rayuwa bayan sauka daga karagar mulki.
- Shugaban Tsimi Da Tanadi Ya Warware Mishkilar Dimbin Bashin Da Ake Bin Jihar Kaduna
- Masana: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Za Ta Sa A Samu Sabuwar Damar Zamanintar Da Nahiyar Afirka
Daya daga cikin tsare-tsaren da aka yi a fadar shugaban kasa ta ‘Aso Rocka’ shi ne sauyin muhallin shugaban kasa da iyalinsa daga babban gidan shugaban kasa na fadar zuwa wani gid ana musamman da ake ce wa ‘Gidan Gilashi’, watau ‘Glass House’. Wani gida ne da aka kebe wa shugaban kasa mai barin gado inda zai koma ya zauna na kwanakin karshe na barin mulkinsa har zuwa ranar da za a rantsar da sabon shugaban kasa.
Idan za a iya tunawa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a lokacin da take zagayawa da uwargidan zabbaben shugaban kasa mai jiran gado a makon da ya gabata, ta bayyana cewa tuni ita da maigidanta shugaba Buhari suka koma Gidan Gilashi inda za su zauna har ranar da za a kaddamar da sabuwar gwamnati, daga nan kuma su zarce Daura ta Jihar Katsina, mahaifar Shugaba Buhari.
Haka kuma, bisa al’adar shirin karbar ragama, bayan tabbatar da nasarar sabon shugaban da za a mika wa ragamar mulki, zabbaben shugaban kasa kan koma wani gidan da aka yi wa lakabi da ‘Gidan Tsaro’, watau ‘Defense House’ da ke unguwar Maitama Abuja, inda a nan zai zauna ya rika shirye-shiryen bikin rantsar da shi.
Tsarin da aka yi na komawar shugaban kasa mai barin gado zuwa gidan gilashi daga asalin gidan shugaban kasa na fadar gwamnati, wani shiri ne da sojoji ke kira “Tactical withdrawal” watau janyewa a sannu a hankali.
Zama a wannan gidan yana da hikimomi kamar guda biyu, zai samar wa da shugaba mai barin gado wajen zama a yayin da ake sake yi wa gidan shugaban kasa kwaskwarima don ya yi daidai da yadda zababben shugaban kasa da mutanesa ke so.
Shugaba mai barin gado zai ci gaba da zama a gidan gilashi har zuwa lokacin da zai kammala wa’adin mulkinsa.
Babban aikin gidan gilashi shi ne, ya kasance wurin da shugaban kasa mai barin gado zai zauna ya kammala tsare-tsaren mika mulki tsakaninsa da gwamnati mai kamawa. Bayan an kadamar da sabuwar gamnati, ba za a sake amfani da gidan ba sai zuwa lokacin da aka samu sabon shugaba da za a mika wa gama.
Wannan wata al’ada ce ta dora Nijeriya a turbar mika mulki ga gwamnati mai shigowa ckin kwanciyar hankali.
A wasu bangare kuma ana ci gaba da tarurruka na a tsakanin wakilan gwamnati mai barin gado da gwamnati mai kamawa domin ganin shirye-shiryen mika ragamar mulkin sun kankama ba tare da kama hannun yaro ba. Har ila yau, duk dai a Abujar, an shirya horaswa ga sabbin ‘yan majalisa da sabbin gwamnoni da gwamnonin masu barin gado kan hanyoyin da za a yi aiki tare domin samun nasarar mika ragamar mulki da kuma yadda sabbon shugabannin da aka zaba za su fara da kafar dama.