An dade ana ce-ce-ku-ce game da dimbin bashin da ake ganin Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya ci wa Jihar Kaduna har ya wuce misali, kan haka wakilinmu SULAIMAN IBRAHIM ya tattauna da Shugaban Hukumar Tsimi da Tanadi ta Jiahar Kaduna, HON. MUHAMMAD JALAL domin ya warware mishkilar da ke tattare da cin bashin. Har ila yau, tattaunawar ta tabo batutuwa da suka shafi sauran sassa na jihar da sha’anin mu’amalar banki a Arewa da sauransu. A karanta har karshe a ji yadda ta kaya a tsakaninsu kamar haka:
A takaice, da wa muke tare…
Muhammad Jalal, Shugaban hukumar ‘Fiscal Responsibility Commission’ a Hausance ‘Hukumar Tsimi Da Tanadi Da Kuma Tabbatar Da Ana Tafiyar Da Kudaden Gwamnati A Kan Ka’ida ta Jihar Kaduna.
An haife shi ne a a shekarar 1968 a Zariya, na yi karatu a makarantu daga Firamare zuwa Sakandire a makarantu daban-daban sakamakon sauyin wurin aiki da ake yi wa Mahaifina, don haka, na shiga makarantar Firamare da Sakandire har sau hudu-hudu, sannan na shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi Digiri na farko da na biyu (Masters) a bangaren Ilimin taswirar gine-gine (Architecture), sannan na yi hidimar kasa a Jihar Enugu, bayan Kammala hidimar kasa, sai na fara aiki da wani kamfanin gine-gine a cikin Jihar Kaduna, ba jimawa na samu canjin aiki zuwa bangaren banki inda na fara da bankin Afri Bank na kusan tsawon shekaru bakwai, sannan na koma Diamond Bank zuwa Sabana Bank, sannan zuwa Eco Bank, daga nan sai na ajiye aikin banki na koma harkokin siyasa.
Ka yi magana a kan hukumarku da ke kula da tsimi da tanadi kan kashe kudaden gwamnati, ko ta wane bangare ne ta yi tasiri a Jihar Kaduna?
Takaitaccen tarihi wannan hukuma ta tsimi da tanadi, tun zamanin Olusegun Obasanjo lokacin yana shugaban kasa aka yi kokarin fara kafa ta a matakin tarayya, lokacin an lura cewa lallai akwai bukatar sanin yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati, ya fara amma bai gama ba sai zuwan Marigayi Shugaba Alhaji Umaru Musa ‘Yar’adua a shekarar 2007, ya kafa ta a matakin tarayya sannan aka ce jihohi kowacce suna iya kafa irin wannan hukuma saboda za ta taimaka wajen sanin inda ake kashe kudaden gwamnati, jihohi sun yi ta kokarin kafa irin wannan hukuma amma a Jihar Kaduna ba a samu wannan nasarar ba sai a zuwan gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i, shi kuma bai hau gwamnati ba sai da ya shirya duk manufofinshi da yake son aiwatarwa, don haka hukumar ‘Fiscal Responsibility Commission’ a Hausance ‘Hukumar tsimi da tanadi da kuma tabbatar da ana tafiyar da kudaden gwamnati a kan ka’ida ta Jihar Kaduna’ da ‘Peace commission’ ma’ana hukumar tabbatar da zaman lafiya suna daya daga cikin hukumomin da ya fara kafawa. An fara mulki a shekara 2015, a 2016 an samar da doka da za ta samar da hukumar ‘Fiscal Responsibility Commission’, a 2017 hukumar ta fara aiki.
Hukumar ‘Fiscal Responsibility Commission’ hukuma ce da ke sa ido a kasafin kudi, duk kudaden da aka ware na aiwatar da wasu ayyuka, za mu sa’ido mu tabbatar cewa, wannan kudin da aka ware, zai isa a kammala ayyukan ko kuma ya zarce kiyasi ko kuma bai kai kiyasi ba, sannan kuma da aka zo fara aikin, nawa aka bayar kuma ina aikin ya tsaya, duk wannan suna daga cikin ayyukan wannan hukuma.
Idan muka ce an samu ci gaba ko kuma an samu nasarori a kan yadda aka tafiyar da kudaden Gwamnatin Jihar Kaduna, ban yi tsammanin akwai wanda zai yi jayayya ba. Saboda duk abin da za ka aibanta wannan gwamnati ta Malam Nasir El-Rufa’i, ba za ka aibantata da satar kudade ba domin kowa ya ga abin da aka yi da su, wannan su ne nasarorin da aka samu kan kafa wannan hukuma.
Kamar yadda na ce maka jihohi da dama sun kafa wannan hukuma amma a Arewa maso Yamma, Jihar Kaduna ce farko, sai kuma daga bayanan kamar Jihar Sokoto a watan Disambar shekarar 2022 ta yi kokarin kafa nata, a Jihohin Kebbi da Jigawa, kudurin kafa hukumar ya tsallake majalisar dokokin jihar amma ba su kafa hukumar ba, sauran Jihohi kamar Kano da Katsina ba su yi komai ba a kan tanadin kafa hukumar.
Ganin cewa, Hukumarku ce ke kula da adadin kudaden da ake kashewa a wurin aiwatar da ayyuka, ko wane aiki ne ya fi cin kudi a gwamnatin El-Rufa’i?
Gaskiya yana da wuya a ce ga aikin da ya fi cin kudi, yadda abin yake koma meye, ya danganta da me za a yi da kudin shi ne. Kamar misalin shirin sake raya birane (Urban renewal), Kaduna ba ta taba samun wani ci gaba kamar wanda aka samu a cikin shekara ukun nan da suka gabata ba, akwai ayyuka da ya dace a yi da yawa na raya birni, ka ga ana bukatar zuba kudade masu yawa, amma kuma in mun koma bangaren Ilimi, da yawan mutane ba su san ayyukan da aka yi a bangaren ba, ka ma daga gyara makarantu, horas da malamai, an kawo kayan aiki, an samu karin yawan dalibai a makarantu, da ana samun sabbin dalibai miliyan daya amma yanzu an haura miliyan biyu a shekara, a makarantu.
A bangaren kiwon lafiya, Jihar kaduna tana da Hukumar Asibitocin Kula Da Lafiya A Matakin Farko (Primary Health care) guda 255, dukkansu babu wanda ba a yi masa kwaskwarima ba kuma an sa masa sababbin na’urorin wutar lantarki masu amfani da hasken rana (Solar), don haka, Gwamnatin Kaduna ta kashe kudade masu yawa a wurin aiwatar da ayyukanta amma bangaren sabunta birni ya fi cin kudi.
Da yake kana da kwarawa a fannin banki, me mutanen Arewa kake ganin ya kamata su sani wanda har yanzun ba su sani ba game da mu’amala da banki wurin bunkasa kasuwanci ko kawo wa kansu ci gaba?
Abin da ya kamata mutanenmu na Arewa su sani shi ne, ba wata rayuwa da ta bunkasa ba tare da amfani da harkar Banki ba, Arewa yanzun za mu iya cewa, tana da bankuna biyu ne kadai – Bankin Ja’iz da Taj, da akwai Bankin Unity, saboda wasu bankunan Arewa suna cikinsa kamar Bank of the North, Intercity da Tropical commercial bank na Kano amma yanzun gudanarwar Bankin ta koma hannun gwamnatin Ribas saboda tsabar kudin da suka zuba a Bankin, yanzu haka, Manajan Darakta na bankin Unity ba dan Arewa ba ne, Bank of the North ya bar Arewa.
Yanzu babu wata harka da za ka yi sai da banki ko da bangaren addini ne, zuwa aikin Hajji dole ka biya kudin a banki, harkar banki bai kamata Arewa ta yi wasa da ita ba, muna da yawa, attajiran masu kudi na Afirka, akwai Aliko Dangote na daya sannan muna da Abdussamad Rabiu BUA, amma ba mu da banki, duk ma’aikatan banki da suka fito daga Arewa, suna da iyaka, akwai mukamin da za a kai dole sai masu bankin ne za su rike mukamin.
A cikin tsare-tsare da banki ke da shi, kamar bangaren bayar da bashi, da hada hannu a yi kasuwanci, ta ina ne aka bar mutanan Arewa a baya, ta inda ya kamata a ce yanzun sun shiga an dama da su?
Banki yana ba da dama a yi kasuwanci, amma mu a wannan bangare saboda harkar ruwa (Interest) ya sa an samu ja baya sosai, sai ka ga mutum dan kasuwa yana alfahari cewa shi da kudinsa kadai yake kasuwanci, wannan kuma zai tauye ci gaban da ya kamata dan kasuwan ya samu, saboda kudin dan kasuwa bai taka kara ya karya ba, amma in ka samu kudin da ba naka ba ka kara cikin kasuwancinka, lallai wannan zai bunkasa maka kasuwancinka, banki yana da kudi masu yawa. Alhamdulillah, kasancewar Sanata Uba Sani ya shugabanci kwamitin gudanar da harkokin banki da kudade na majalisar tarayya, ya taimaka wa Arewa da abubuwa masu yawa, akwai wasu tallafi masu yawa da ke fitowa daga babban bankin Nijeriya (CBN) da wasu bangarori da ke jikin bankin, sannan kuma akwai wasu sharuda da suke hana ‘yan Arewa samun wadannan basussukan. Kamar misali a wancan lokacin, in za a ba ka bashi sai ka kawo tarihin asusun bankinka da wanda zai tsaya maka ko kuma ka bayar da wata kadara babba, amma duk wadannan sharuda, Sanata Uba Sani ya sa aka kawar da su saboda ‘yan Arewa, Alhamdu lillah, ‘yan Arewa sun samu irin wannan tallafi da yawa, sai dai Allah ya sa sun yi amfani da bashin ta yadda ya dace. Arewa ba ta da abu sama da noma, nan ma akwai ja-da-baya sosai, wasu kuma sai su amsa kudin amma sai su yi wani abu daban da kudin wanda hakan bai dace ba, wannan bangaren ya kamata ‘yan Arewa su yi amfani da shi sosai, ya kamata a wayar wa ‘yan Arewa da kai sosai, kamar ta hanyar amfani da kungiyoyin Arewa – Arewa consultatibe Forum da Arewa Northern elders, ba wai kawai su takaita kansu kan harkokin siyasa ba kadai.
Ko za ka dan yi tsokaci game da Jihar Kaduna a karkashin mulkin Gwamna El-Rufa’i?
Gaskiya an samu ci gaba sosai, Kaduna ta samu ci gaban da ba ta taba samu ba, akwai wani wasan ba’a da ake yi wa Kaduna cewa “Da Sardauna zai dawo Kaduna, da zai kai kanshi gida da kansa”, amma yanzun wannan kakacin ko ba’a ba zai taba zama gaskiya ba. Akwai wani mazaunin Kaduna da ya yi tafiya ta wata Biyu, da ya dawo sai da ya yi tambaya sannan aka nuna masa inda za shi. Wannan ci gaba ne da al’ummar Jihar Kaduna ke alfahari da hakan, kuma muna sa ran, gwamna mai jiran Gado, Sanata Uba Sani zai dora daga inda Gwamnatin Malam Nasir ta tsaya.
Ko za mu iya sanin adadin kasafin kudaden da gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i ta yi daga farkon Mulki har zuwa kasafin 2023?
To, a shekarar 2015 an yi kasafin Naira biliyan 205, a 2016 an yi na Naira Biliyan 173, a 2017 Naira Biliyan 215, sai 2018 da aka yi na Naira Biliyan 217, kana a shekarar karshen wa’adin mulki na farko, 2029 aka yi kasafin Naira Biliyan 157.
A 2020, Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufa’i ta yi kasafin Naira Biliyan 259, a 2021 ta yi na Naira Biliyan 205 sai 2022 da aka yi na Naira Biliyan 259 sannan a wannan shekara ta 2023, an yi kasafin Naira Biliyan 376.
A bangaren kudin shiga kuma, Gwamnatin el-Rufa’i a shekarar farko, 2015, an samu kudin shiga Naira Biliyan 15 da wasu daruruwa, amma yanzun a shekarar da ta gabata kadai, 2022, an samu kudi kusan Naira Biliyan 77, duk shekara ana samun karuwa kan kudin shiga, saboda wannan nasara, jihohi da dama har da su Kano sun zo Kaduna suna tambaya me ke faruwa ne. Kaduna ita ce a mataki na 6 kan samun kudin shiga a Nijeriya kuma ta daya a Arewa duk da cewa kasuwancin da ke Kaduna bai kai na wasu Jihohin ba, Jihohi kamar Kano, Borno, Filato sun fi Kaduna yawan Kasuwanci, abin mamaki shi ne, duk wannan ci gaba da Jihar Kaduna ta samu, ba ta kara yawan haraji ba, ba ta kirkiro wani sabon haraji ba wanda da babu shi, abin da kawai aka yi shi ne, an tottoshe wuraren da kudaden jihar ke zubewa, dama akwai kudaden, zurarewa kawai suke yi, daya daga cikin hanyoyin da aka bi shi ne, mayar da asusun gwamnati daya (Treasury single account), wannan tsarin bai yi wa wasu ma’aikata dadi ba saboda ‘yan hanyoyin da suke bi wurin almundahana an tottoshe, wannan shi ya sa wasu jihohin ba za su iya aiwatar da wannan tsari ba.
Da yawa suna ganin Gwamnatin Kaduna ta ci bashin da ya fi karfinta, ana ganin Malam Nasir ya gadar wa Uba Sani bashi fiye da karfin jihar, me za ka ce game da hakan?
Bari in fara da cewa, kafin zuwan El-Rufa’i, Kaduna ita ce ta biyu a bashin kasar waje bayan Legas, amma me aka yi da bashin, Kokarin janyo Ruwan Zariya, Allah kadai ya san adadin kudin bashin da aka amso amma komai ba a yi ba, da Malam Nasiru El-Rufa’i ya amsa mulki, duka bashin da ya amsa Dala Miliyan 350 ne kawai amma kowa ya ga aikin da aka yi. Masu cewa an ci bashi da yawa sam ba haka ba ne, saboda masu ba da bashin su ba mahaukata ba ne, ba za su ba ka bashin abin da suka san ba za ka iya biya ba, sai sun tabbata za ka iya biya, ana zuwa matakin da suka san ba za ka iya biya ba za su janye hannunsu. Tun da ka ga sun bayar da bashin kuma yanzun haka an fara biyan bashin, kuma babu wanda ya ji cewa an kasa biyan albashi ko kuma ayyukan da ake malalawa sun tsaya kuma ba wai wani sabon bashin aka kara amsowa ba, kawai an samu karin kudin shiga ne (IGR), lallai bashin da aka amso yana da yawa amma bai fi karfin Jihar Kaduna ba da za a ce ba za ta iya biya ba.
Kamar cikin Shekara nawa Jihar Kaduna za ta biya basussukan da ta amso?
Ya danganta da yarjejeniyar da aka yi wurin amso bashin, akwai wanda aka yi za a biya cikin shekara biyar, wani cikin shekara 10, akwai wanda ba ma yanzun za a fara biya ba sai nan da shekara 10, abin alfahari da wannan bashin da aka samu shi ne, Bankin Duniya ne ya ba da lamunin. A Afrika, Bankin Duniya bai taba ba da bashi mai sauki irin wanda ya ba Jihar Kaduna ba, kudin ruwan da suka bayar 0.05 cikin kashi 100, sannan kuma sai nan da shekara 10 za a fara biya, don haka wannan ba wani bashi ne da zai damu Jihar Kaduna ba.
Kana aiki a karkashin gwamnati mai ci a kuma ana sa ran za a tafi da kai a sabuwar gwamnati mai zuwa, ya kake hasashen gwamnatin Malam Uba Sani za ta kasance a Jihar Kaduna?
Malam Uba Sani ya taka rawa mai yawa a cikin Gwamnatin Malam Nasiru, shi ne mai bayar da shawara kan harkokin siyasa a Jihar Kaduna, da kuma ya tafi Sanata, shi ne Sanata daya wanda ya tsaya tsayin daka kan abin da suka shafi Jihar Kaduna, saboda haka, Sanata Uba Sani ba bako ba ne, kawai zai zo ne ya ci gaba daga inda aka tsaya a Jihar Kaduna, sannan kuma muna cikin wannan gwamnati, ba yadda za a yi a ce ba za mu bashi shawara ba kan abubuwan da muka ga ya dace a yi gyara ba. Wannan babban tarihi ne a Jihar Kaduna cewa an samu canjin gwamnati amma ba za mu san an samu canjin ba saboda komai zai ci gaba a kan tsari.
Da yawa a kan samu sabani tsakanin gwamna mai barin gado da kuma gwamna mai jiran gado musamman wajen nade-naden mukamai a gwamnati, kuma ya sha faruwa wanda hakan kan shafi ci gaban Jiha, a Kaduna mai kake tunani game da irin wannan?
Gaskiya ne irin hakan yakan faru, saboda siyasa ce ta hada mai jiran gado da mai barin gado, amma su wadannan akwai wani aminci da zumunci da ke tsakaninsu fiye da shekara 25, ba yau suka fara ba, saboda haka, ba siyasa ce kadai ta hada su ba, akwai abokantaka, akwai aminci da amana. Abubuwan da Malam Uba Sani Ya yi ma Malam Nasir el-Rufa’i lokacin da ya bar Nijeriya don neman mafaka a kasashen waje, abubuwa ne masu yawa, yana Sanata ya dauko Babban Dan Malam Nasiru, ya bashi mukamin shugaban ma’aikatansa, kuma sannan ya taimake shi ya tsaya takara har ya samu nasara a kujerar da ya nema, in sha Allah ba na tunanin za a samu irin wannan sabani na tsakanin gwamna mai jiran gado da mai barin gado.
Kana daya daga cikin kwamitin karbar Mulki, mene ne kwamitinku yake yi tun da wannan kamar gwamnati ce mai ci gaba kawai?
Akwai kwamiti babba na amsar mulki, a karkashinsa an yi kananan kwamitoci har guda tara, kowanne da irin aikin da aka bashi, amma ni saboda bangaren da na karanta, harkar gine-gine ne, ina cikin kwamitin da zai kula da aikace-aikace (Infrastructure), don haka, muna duba ma’aikatun da suka yi duk wasu aikace-aikace, kamar ma’aikatar ayyuka da gidaje, ma’aikatar raya birane, KASUPDA, KSDPC, Hukumar Kula da Ruwa, da KASTELEA da dai sauransu. A takaice, Ma’aikatu biyu ne da hukumomin da suke karkashinsu aka ba mu kula da su (Ministry of public works and housing da Ministry of housing and Urban debelopment) muna duba ayyukan da suka yi, muna duba rubutun da suka yi na barin ofis don shirya wa gwamnati mai zuwa, in ta shigo ta san daga inda za ta ci gaba, wannan shi ne ayyukan da muke yi, amma akwai kwamitin da aka ba wa bangaren kiwon lafiya, akwai masu kula da bangaren da suka shafi tattara kudade, akwai masu bangaren Ilimi da dai sauransu.
Ko akwai abin da za ka so ka bayyana wa masu karatu wanda ba mu tambayeka ba?
Alhamdulillah… abin da zan ce kawai shi ne, wannan sabuwar gwamnati ta malam Uba Sani tana neman goyon baya kamar yadda aka mara wa gwamnatin Malam Nasir baya, ina yi muku alkawari da alfaharin cewa, ina baku tabbacin cewa, ba za a samu matsala ba, a wannan sabuwar gwamnatin. Kamar yadda Malam Nasiru ke fada cewa, shi dan’adam ne kuma ajizi, akwai abubuwan da bai yi ba amma Insha Allah Malam Uba Sani zai yi. Kauyuka suna korafin cewa, Malam Nasir bai musu ayyuka ba amma Malam Uba Sani ya ce zai shiga kauyuka, duk da cewa babu wata karamar hukuma da ba a yi mata komai ba a wannan gwamnati, ko dai an musu abin da ya shafi makaranta ko asibiti ko titi, in ka je Kachiya da Soba duk manyan titunansu an yi musu. Babban albishir da zan yi wa mutanen Kaduna shi ne, mun yi zaben da ya dace, kuma In Allah ya yarda za a gani. Kowa ya karanta tarihin Malam Uba Sani, shi ya sa har aka zabe shi. Abin da aka fara ba za a fasa ba, za a ci gaba da dorawa kan inda aka tsaya. Alhamdu lillah!