Tsohon Hafsan Hafshoshin sojin kasa kuma Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Benin Laftanar-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya sanar da cewa, yana da kwarin gwiwa Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kawo karshen kalubalen rashin tsaro da Nijeriya ke ci gaba fuskanta.
Buratai ya kuma roki ‘yan Nijeriya da su kara yin hakuri kan kokarin da Gwamnatin ke ci gaba da yi Na lalubo bakin Zaren dangane da kalubalen na rashin tsaron.
- Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
Ya sanar da hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin wata kungiyar da ke sa ido a kan tsaro a nahiyar Afirka da ake kira da Security Watch Africa (SWA).
Shugaban kungiyar Mista Patrick Agbambu ne ya jagoranci kungiyar a lokacin ziyarar.
A cewar Buratai, baya ga magance kalubalen ‘yan ta’adda a yankin Arewa Maso Gabas, Gwamnatin ta Buhari Na kuma kan yin kokarin magance kalubalen masu garkuwar da mutane da ta’addanci da sauran aikata manyan laifuka a kasar nan Buratai ya ci gaba da cewa, na yi imani da cewa, Gwamnatin Buhari ta damu matuka kuma ba wai ta rungume hannunta bane kan kalubalen na rashin tsaro a kasar nan ba, inda ya kara da cewa, bisa tsoron da ke a ciki zukantan ‘yan kasar abu ne da ban ba da dade wa zai gushe.
Ya ya nuni da cewa, lamarin na rashin tsaron kafin zuwan Gwamnatin Buhari abu ne da ya munana, amma bayan da Buhari ya dare Karagar shugabancin kasar a shekarar 2015, muna gode wa Allah kan canjin da Buhari ya samar kan rage kalubalen.