A jiya Jumma’a 13 ga watan Janairun nan ne shugaban kasar Benin Patrice Talon, ya gana da ministan harkokin wajen Sin Qin Gang, a birnin Cotonou fadar mulkin kasar.
Yayin da suke zantawa, shugaba Talon ya bukaci Mr. Qin Gang da ya mika gaisuwar sa ta musamman, da fatan alheri ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, yana mai cewa, sabon ministan harkokin wajen Sin ya ziyarci Benin a ziyarar sa ta farko a Afirka, jim kadan bayan da Sin da Benin suka yi bikin cika shekaru 50 da maido da huldar diflomasiyya tsakanin su, wanda hakan ke shaida kawance, da kusancin kut da kut dake tsakanin su.
Kaza lika shugaba Talon ya ce “Muna martaba goyon baya, da tallafin da Sin ke ba mu a tsawon lokaci. Duk da cewa Benin karamar kasa ce, za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka da kasancewa abokan Sin na hakika, bisa goyon bayan gaskiya, da daidaito da adalci.
A nasa bangare kuwa, Qin Gang ya mika sakon gaisuwar shugaba Xi ga shugaba Talon, yana mai godewa Benin bisa fahimta, da goyon baya da take nunawa kasar Sin a muhimman manufofin ta, da manyan abubuwan da take mayar da hankali a kan su.
Qin ya kara da cewa, Sin a shirye take wajen ci gaba da yin kawance a fannin siyasa da wanzar da ci gaba. Ya ce “Burin mu shi ne aiwatar da muhimman kudirori da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, da sakamakon shawarwarin da aka amincewa, yayin taro na 8 na ministocin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, tare da daga matsayin shawarar ziri daya da hanya daya zuwa mataki na gaba.
Yayin ziyarar ta Qin Gang a Benin, ya tattauna da takwaransa na kasar Aurélien Agbenonci. Jami’an 2 sun kuma sanya hannu kan kundin hadin gwiwar kasashen su. (Saminu Alhassan)