Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da ƙudirin sauya Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo, dake Jihar Kano. Wannan mataki, a cewarsa, babban ci gaba ne wajen bunƙasa ilimi da fasaha a Nijeriya.
A zaman majalisar dattawa na ranar Talata 27 ga Mayu 2025, an karanta takardar Shugaban Ƙasa wacce ta bayyana amincewarsa da kafa jami’o’i uku a jihohin Kano, Akwa Ibom da Oyo. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar yayin zaman.
- Babu Wasu Masu Juya Tinubu Ta Bayan Fage – Ministan Yaɗa Labarai
- Gwamnatin Kano Zata Gina Masallacin Da Aka Ƙona Masallata A Gezawa
Sanata Barau, wanda shi ne ya ɗauki nauyin ƙudirin dokar, ya bayyana cewa kafa wannan jami’a zai ƙara damar samun ilimi ga matasa tare da samar da ƙwarewa da ilimin fasaha da zai taimaka wajen gina ƙasa.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya bayyana cewa ilimi shine tushen ci gaban kowace al’umma. Ya ce matasa ne ginshikin gina ƙasa, don haka duk wani mataki da zai taimaka musu yana da matuƙar muhimmanci.
A ƙarshe, Sanata Barau ya gode wa Shugaba Tinubu bisa hangen nesansa na bunƙasa harkar ilimi da kimiyya, yana mai cewa wannan mataki zai kasance gagarumin ci gaba ga al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp