Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro a fadarsa da ke Abuja a yau Litinin, domin tattauna sabbin matakai na ƙarfafa tsaron ƙasa.
Taron, wanda aka gudanar ƙofa kulle, ya biyo bayan naɗin sabbin shugabannin rundunonin Soji da aka yi kwanan nan. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana wannan mataki a matsayin wani ɓangare na gyaran tsari don ƙara ƙwarewa, da inganci, da ƙarfafa gwuiwar jami’an tsaro.
- Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu
- Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Olufemi Oluyede; Babban Hafsan Sojin Ƙasa, da Manjo Janar Waheedi Shaibu; Babban Hafsan Sojin Sama, da Air Vice Marshal Kennedy Aneke; da Babban Hafsan Sojin Ruwa, da Rear Admiral Idi Abbas.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanan tattaunawar tsakanin Shugaba Tinubu da sabbin hafsoshin tsaron ba, sai dai majiyoyi sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ƙalubalen tsaro da kuma sabbin dabarun haɗin kai tsakanin rundunonin Soji.
Cikakkun bayanai za su biyo baya…














