Shugaba Bola Tinubu, a ranar Alhamis, ya rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro.
An gudanar da bikin rantsar da Janar Musa (mai ritaya) ne kasa da awanni 24 bayan Majalisar Dattawa ta tantance shi kuma ta tabbatar da nadinsa.
Tinubu ya tura sunan Musa ga Majalisar Dattawa a farkon makon nan bayan murabus ɗin Mohammed Badaru, wanda ya sauka daga mukaminsa na Ministan Tsaro bisa dalilai na lafiya.
Naɗin Musa ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar, inda gwamnati ke nufin amfani da ƙwarewarsa ta soja don ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta’addanci da tsaron cikin gida.














