Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa yankin Macao ta jirgin saman musamman da yammacin yau 18 ga wannan wata, inda zai halarci bikin cikar yankin Macao shekaru 25 da dawowa kasar Sin, da bikin kaddamar da gwamnatin yankin Macao ta 6, tare da yin rangadin aiki a yankin.
Bayan isarsa, shugaba Xi ya gabatar da jawabi a filin jirgin sama yana cewa, a cikin shekaru 25 da suka gabata, an aiwatar da manufar Sin daya mai tsarin mulki biyu a yankin Macao, wadda kuma ta samu nasara. Ya ce an samu ci gaba a fannoni daban daban a kasar Sin, ana kuma da kyakkyawan fata ga makomar yankin Macao. A cewarsa, wannan abun alfahari ne ga jama’ar yankin Macao da kuma baki dayan jama’ar kasar Sin. Ya ce ya yi imanin cewa, idan aka ci gaba da aiwatar da manufar Sin daya mai tsarin mulki biyu a yankin tare da kokarin yin kirkire-kirkire, to za a samu kyakkyawar makoma a yankin Macao. (Zainab Zhang)