A ranar Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos, ga shugaban kasar mai ci João Manuel Gonçalves Lourenço.
Cikin sakon nasa, a madadin gwamnati da daukacin al’ummar kasar Sin, shugaba Xi ya bayyana matukar kaduwa da jin labarin rasuwar Mr. Eduardo dos Santos, yana mai bayyana tsohon shugaban na Angola a matsayin dadadden aboki ga al’ummar kasar Sin, wanda kuma ya yi matukar kokari wajen bunkasa ci gaban alakar kasarsa da kasar Sin.
Xi ya kuma bayyana gamsuwa ga kawancen gargajiya tsakanin kasar sa da Angola, yana mai fatan ci gaba da aiki tare da bangaren Angola, wajen fadadawa, da zurfafa hadin gwiwar kawancensu a dukkanin bangarori, tare da ingiza alakar hadin kan sassan 2, zuwa muhimmiyar alakar abota da za ta amfani kasashen da al’ummunsu. (Saminu)