Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude dandalin tattaunawa tsakanin al’ummun gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan karo na 15.
Cikin wasikar da ya aike ga dandalin a Asabar din nan, shugaba Xi ya ce
za a ci gaba da martabawa, da nuna kulawa, da samar da tarin alherai ga ‘yan uwa mutanen Taiwan. Kaza lika za a goyi bayan musaya a fannonin tattalin arziki, da musayar al’adu, da hadin gwiwa, baya ga ingiza ci gaban bai daya a fannoni daban daban.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummun Taiwan da na babban yankin kasar Sin, da su yi aiki tare wajen kare martabar tarihin su, da kare daukacin moriyar kasar Sin, su kuma ba da gudummawar wanzar da ci gaban alakar sassan cikin lumana, tare da ingiza dunkulewar kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp