Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron kasa da kasa game da tsaffin al’adun wayewar kan al’umma, wanda aka bude yau Alhamis a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Cikin sakon nasa ga taron, wanda aka yiwa lakabi da “Tsaffin al’adun wayewar kan al’umma da duniyar zamanin yau”, shugaba Xi ya ce, taron na wannan karo, wanda kasashen Sin da Girka ke daukar nauyi, tare da tsangayar nazarin tsaffin al’adun wayewar kan al’umma dake birnin Athens da aka kafa, ya samar da wani sabon dandali na musayar al’adun wayewar kai, da koyi da juna tsakanin Sin da Girka da ma sauran sassan kasashen duniya. (Saminu Alhassan)