Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya rattaba hannu kan wani umarnin bayar da lambobin yabo na kasa da shaidar karramawa ga wasu daidaikun mutane 15, albarkacin cikar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin shekaru 75 da kafuwa.
Umarnin na zuwa ne bayan kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya kada kuri’ar amincewa da matakin karramawar, yayin wani taro a yau din.
- Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Murnar Budewar Dandalin Xiangshan Na Beijing Karo Na 11
- Sin Na Shirin Soke Daukacin Haraji Kan Hajojin Dake Shiga Kasar Daga Kasashe Mafiya Karancin Wadata
Daga cikin mutanen, 4 sun samu lambar yabo ta Jamhuriyar Kasar, wadanda suka hada da marigayi Wang Yonzhi, masanin hada makaman roka da na linzami, kuma mutum na farko da ya tsara shirin kumbon da ke daukar ’yan sama jannati na kasar Sin da Wang Zhenyi, masanin kimiyyar kiwon lafiya da ya samu gagarumar nasara wajen maganin cutar sankarar bargo ta Leukemia da Li Zhensheng, kwararre kan noman alkama mai aure da Huang Zongde, tsohon sojin da ya shiga yake-yaken da kasar ta yi.
Har ila yau, an bayar da lambar yabo ta abota ga Dilma Rousseff, shugabar sabon bankin raya kasashe kuma tsohuwar shugabar Brazil.
Kana sauran mutanen 10, sun samu shaidar karramawa ta kasa. (Fa’iza Mustapha)