Wata sanarwa da ofishin lura da buga harajin kwastam na majalissar gudanarwar kasar Sin ya fitar, ta ce tun daga ranar 1 ga watan Disamban karshen shekarar nan ta 2024, Sin za ta fara aiwatar da manufar soke daukacin haraji kan hajojin dake shiga kasar daga kasashe mafiya karancin wadata da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar.
Sanarwar ta ce gwamnatin Sin za ta aiwatar da wannan manufa ne domin taimakawa ci gaban bai daya na dukkanin sassan duniya. (Saminu Alhassan)
Talla
Talla