Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyarsa ta aiki tare da kasar Rasha, don karfafa taimakon juna kan batutuwan dake shafar babbar moriyar sassan biyu.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin da yake zantawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, jiya Alhamis a babban ginin Forumlar Majmuasi na birnin Samarkand dake kasar Uzbekistan.
Shugabannin biyu sun gane domin yin musaya, game da batutuwan da suka shafi kasashensu a mataki na kasa da kasa da na shiyyoyi. Xi ya ce a wannan gaba da duniya ke fuskantar sauye-sauye, Sin za ta yi aiki tukuru tare da Rasha, don sauke nauyin dake wuyansu, a matsayin su na manyan kasashe, za su kuma yi rawar gani wajen ingiza samar da daidaito, a duniya dake fama da sauyi da rashin daidaito.
A nasa bangare kuwa, shugaba Putin ya yiwa JKS fatan samun nasara a babban taron ta karo na 20 da za a shirya a wata mai zuwa. Yana mai imanin cewa, karkashin jagorancin shugaba Xi, Sin za ta ci gaba da cimma manyan nasarori a fannin tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Shugaban na Rsaha ya kara da cewa, duniya na fuskantar manyan sauye sauye, amma duk da haka, kawance da aminci dake tsakanin Sin da Rasha bai sauya ba.
Kaza lika sassan biyu na ci gaba da raya cikakken hadin gwiwa dake tsakaninsu yadda ya kamata. Ya ce Rasha da Sin, sun amince da bin tsarin gudanar da duniya mai ma’ana bisa adalci, suna kuma kafa misali na kyakkyawan hadin gwiwar kasa da kasa ga duniya.
Baya ga shugaba Putin, shugaba Xi ya kuma gana da shugaban kasar Azerbaijani Ilham Aliyev, da na Belarus Alexander Lukashenko, da na Mongolia Ukhnaa Khurelsukh, da na Iran Seyed Ebrahim Raisi, da na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da kuma firaministan kasar Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif.
Bugu da kari, ya jagoranci taro karo na 6 na kasashen Sin da Rasha da Mongolia a ranar 15 zuwa 16 ga wata. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)