Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun gudanar da taron koli a rukunin gidajen alfarma na Filoli, dake birnin San Francisco na kasar Amurka jiya Laraba agogon wurin, inda suka yi musayar ra’ayoyi da ma bayanai kan muhimman batutuwa masu sarkakiya dake da muhimmanci ga alkiblar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da manyan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da ci gaban duniya.
Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, ga kasashen Sin da Amurka, juya wa juna baya ba shi ne zabi ba. Ba gaskiya ba ne wani bangare ya sakewa wani bangare fasali. Kuma rikici da nuna adawa na iya haifar da sakamakon da bangarorin biyu ba za su iya jurewa ba.
Haka kuma takarar manyan kasashe, ba za ta iya magance matsalolin da ke addabar Sin da Amurka ko duniya ba. Duniya tana da girman da ƙasashen biyu za su sakata su wala, kuma nasarar wata kasa dama ce ga wata.
Shugaban na kasar Sin ya kuma yi karin haske, kan muhimman sigogin tsarin zamanintar da kasar Sin da ma’anarsa, da ci gaban da kasar Sin ke samu, da kuma manufarta bisa manyan tsare-tsare. Ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana kokarin farfado da al’ummar Sinawa daga dukkan fannoni ta hanyar zamanantar da kasar. Don haka, ba za ta koma kan tsohuwar hanyar mulkin mallaka da kwasar ganima ba, ko kuma hanyar da ba ta dace ba ta neman mulkin danniya da nuna fin karfi. Haka kuma kasar Sin ba ta fitar da akidunta, ko kuma yin adawa da akida da wata kasa ba. Kasar Sin ba ta da wani shiri na maye gurbin Amurka.
Haka kuma, bai dace kasar Amurka ta nemi dakile ci gaban kasar Sin da ma mamaye ta ba.
Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, mutunta juna, da zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwar samun nasara tare, su ne darussan da muka koya daga shekaru 50 na dangantakar kasashen Sin da Amurka, da kuma rikice-rikice tsakanin manyan kasashe a tarihi.
A Bali a shekarar da ta gabata, bangaren Amurka ya bayyana cewa, ba ya neman sauya tsarin kasar Sin, ko fara wani sabon yakin cacar baki, ko sake nuna kiyayya ga kasar Sin, ko goyon bayan ‘yancin kai na Taiwan, ko shiga rikici da kasar Sin.
A San Francisco kuma, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Sin da Amurka su yi sabon hangen nesa tare da gina ginshiƙai biyar tare, don inganta alakar dake tsakaninsu.
Na farko, habaka daidaitacciyar fahimta tare, Na biyu, magance rashin jituwa tare yadda ya kamata. Na uku, ciyar da hadin gwiwar moriyar juna gaba tare, sai na hudu, sauke nauyin dake wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe. Kana na biyar kuma na karshe, shi ne inganta mu’amala tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Shugabannin biyu sun kuma amince da kokarin da tawagoginsu ke yi na tattaunawa kan raya ka’idojin da suka shafi inganta dangantaka tsakanin kasashen biyu tun daga taron Bali.
Sun kuma jaddada muhimmancin dake akwai ga dukkan kasashen duniya, su rika mutunta juna da samun hanyar zaman tare da juna cikin lumana, da kiyaye hanyoyin tattaunawa ba tare da wata rufa-rufa ba, da magance tashe-tashen hankula, da martaba kundin tsarin mulkin MDD, da yin hadin gwiwa a fannonin cin moriyar juna, da yin takara mai tsafa a bangarorin dangantaka.
Haka kuma shugabannin biyu sun yi maraba da ci gaba da tattaunawa dangane da hakan. (Mai fassara: Ibrahim)