Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkun manufofin JKS a jihar Xinjiang, domin cimma nasarar jagorancin jihar a sabon zamani, matakin da a cewarsa zai haifar da daidaito, da yanayin tsaro mai dorewa da ake da buri.
Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake rangadi a jihar ta Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kan ta, dake arewa maso yammacin kasar Sin, tsakanin ranekun Talata zuwa Juma’ar nan. (Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa)