Da yammacin yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci wani taron karawa juna sani a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar, game da bunkasa ci gaban yankin yammacin kasar Sin a sabon zamani.
Cikin muhimmin jawabin da ya gabatar yayin zaman, shugaba Xi ya jaddada cewa, yankin yammacin kasar Sin na taka muhimmiyar rawa, wajen yin gyare-gyare a kasar da samun ci gaba da kuma daidaito.
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Dubi Kanta Game Da Yanayin Kare Hakkin Dan Adam
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai 2 A Kaduna
Ya ce, wajibi ne a aiwatar da manufofi, da matakan kwamitin kolin JKS, ta fuskar ingiza ci gaban yankin na yammacin Sin, kana a kara kafa wani sabon salo na kare kai, da kara bude kofa ga ketare, da samun ci gaba mai inganci, da bunkasa daukacin karfi, da kwarewar bunkasa kai mai dorewa na yankin, a kuma kara azamar bude sabon babi na bunkasa yankin na yammacin Sin, karkashin burin zamanantarwa irin na kasar Sin.
Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Chongqing daga jiya Litinin zuwa yau Talata. Yayin rangadin, Xi ya kai ziyarar cibiyar jigilar kayayyaki ta kasa da kasa, da unguwar mazauna dake yankin Jiulongpo, da kuma cibiyar tafiyar da harkokin birnin ta zamani.
Ya kuma gano kokarin da gwamnatin birnin ke yi wajen gaggauta raya sabuwar cibiyar cinikayya daga kan tudu zuwa teku ta kasa da kasa dake yammacin kasar, da aiwatar da ayyukan sabunta birnin, da tabbatar da kyautata rayuwar jama’a, da ma yunkurin zamanantar da tsarin tafiyar da harkokin birnin.
Kana shugaba Xi Jinping ya ce, walwalar jama’a abu ne mai matukar muhimmanci ga zamanantar da kasar Sin, manufar JKS ita ce, tabbatar da jama’a suna rayuwa cikin farin ciki.
Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, ya zama wajibi a fayyace iko da nauyin da ya rataya a wuyan wadanda suke aiki a matakin farko, domin rage masu nauyi.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci wata unguwa dake yankin Jiulongpo, wadda aka yi wa gyaran fuska kuma take cikin yanayi mai kyau.
Haka kuma, ya ziyarci cibiyar kula da harkokin unguwar, yana mai tambayar ma’aikata ayyukan da suke gudanarwa da albashinsu da yawan ayyukansu, domin fahimtar yadda yunkurin ragewa ma’aikata yawan ayyuka a matakin unguwanni ke yin tasiri a shekarun baya-bayan nan. (Fa’iza Mustapha&Saminu Alhassan)