Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon jaje ga shugaban Myanmar Min Aung Hlaing, game da mummunar girgizar kasa da ta aukawa kasar a jiya Juma’a.
Cikin sakon, shugaba Xi ya ce ya kadu da ya ji labarin mummunan ibtila’in da ya jikkata mutane da dama da haifar da asarar dukiyoyi.
- Sin Da Laberiya Sun Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Ta Fuskar Tattalin Arziki Da Fasaha
- Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi
Ya ce, a madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, yana jimamin mace-macen da aka samu da jajantawa iyalan mamatan da wadanda suka ji rauni da sauran mutanen da ibtila’in ya shafa.
Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta samar da tallafi da goyon baya ga kokarin shawo kan lamarin da sake gina gidaje nan ba da dadewa ba.
Shi ma a yau din, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jajantawa Min Aung Hlaing game da ibtila’in. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp