Da yammacin jiya Talata 10 ga watan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci sashen birnin Jiujiang na yankin raya al’adun kogin Yangtze, da reshen kamfanin Sinopec Jiujiang, wanda ke birnin Jiujiang na lardin Jiangxi na kasar Sin, inda ya ganewa idanun sa yadda ake ginin yankin raya al’adu na kogin Yangtze, da yadda ake kyautata sake farfado da muhallin halittu a gabar kogin Yangtze, da yadda ake kokarin sauya tsarin masana’antun sarrafa albarkatun man fetur ta hanyar kawar da fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da daga matsayin ingancin su.(Saminu Alhassan)