Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Sakatarori guda takwas a yau Laraba kafin fara taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a Fadar Shugaban ƙasa. An gudanar da gajeren bikin rantsarwar ne cikin rukuni biyu, wanda mai ba da shawara na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya jagoranta, tare da karanta tarihin sabbin waɗanda aka nada.
Sabbin Sakatarorin sun haɗa da Dr. Emanso Umobong Okop (Akwa-Ibom), da Obi Emeka Vitalis (Anambra), da Mahmood Fatima (Bauchi), da Danjuma Mohammed Sanusi (Jigawa), da Olusanya Olubunmi (Ondo), da Dr. Keshinro Maryam Ismaila (Zamfara), da Akujobi Chinyere Ijeoma (Kudancin Gabas), da Isokpunwu Christopher Osaruwanmwen (Kudancin Kudu).
- Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa
- Mun Ja Hankalin Tinubu Kan Tsadar Kayan Abinci – Ndume
A lokacin taron, ‘yan majalisar zartarwar sun taya Shugaba Tinubu murna bisa sake zaɓensa a matsayin Shugaban ƙungiyar Ƙasashen tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS). Sakatare ga Gwamnatin Tarayya, Sen. George Akume, ya yaba da himmar Shugaba Tinubu ga ci gaban Nijeriya da Afrika baki ɗaya, inda ya danganta wannan jajircewa da sake zaɓensa da shugabannin yankin Yammacin Afrika suka yi.