Fadar gwamnatin Amurka ta white House ta da sanar cewa, Shugaba Joe Biden ya kamu da cutar COVID 19, jim kadan bayan ya soke gabatar da jawabi a Las Vegas, inda ya shirya zai janyo hankalin al’ummar Latino masu kada kuri’a.
Shugaban mai shekaru 81 a duniya, ya kamu da cutar ne, kafin taron shi na farko a Las Vegas a ran Laraba, inda ya nuna kananan alamun kamuwa da cutar, a cewar jami’ar hulda da ‘yan jarida ta fadar white House, Jean-Pierre cikin wata sanarwa.
- Sin Za Ta Tallafawa Kamfanonin Gida Da Na Waje A Fannin Sabunta Na’urori Da Yin Musayar Tsoffin Kaya Da Sabbi
- IMF Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2024 Zuwa Kashi 5%
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban ya karbi rigakafin cutar har ma da kari, zai kuma koma gidansa da ke Rehhoboth, Delaware, inda zai kebe kansa.
Jean ta ce, Fadar White House za ta rika sanar da halin da shugaban ke ciki, a yayin da yake ci gaba da gudanar da ayyukan ofishinsa a inda yake.
Ta kara da cewa, “Fadar White House za ta rika bayyana halin da Shugaban kasar yake ciki akai-akai , yayin da yake ci gaba da gudanar da cikakken ayyukansa na ofis lokacin da yake a kebe.”
Bayan bayanin na Jean-Pierre, likitan Biden ya ya yi karin bayani cewa, Shugaban kasar yana numfashi yadda ya kamata an kuma ba sa magani.
Likitan, wanda ba a bayyana sunansa ba a cikin sanarwar, ya ce Biden ya nuna alamun da suka hada da mura, da tari da kuma lauyayi.