Shugaban Angola Joao Lurenco, ya yaba sosai da gudunmuwar da tashar samar da lantarki daga ruwa ta Caculo Cabaca da Sin ta gina a kasar ke bayarwa ga bangarorin tattalin arziki da zaman takewa a kasar, yana mai cewa, tashar za ta samar da dimbin alfanu a bangaren samar da makamashi da inganta rayuwar al’ummar Angola.
Joao Lorenco ya bayyana haka ne ranar Asabar a lardin Cuanza Norte dake arewa maso tsakiyar kasar, yayin da ya halarci bikin karkatar da ruwan kogin Cuanza na wucin gadi, daya daga cikin kogunan kasar mafi tsawo, wanda ya alamta fara aikin ginin babban bangaren tashar ta samar da lantarki daga ruwa. Bayan kammaluwarta, tashar za ta kasance irinta mafi girma a Angola, kana ta 3 a nahiyar Afrika.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da makamashi da ruwa na kasar, Jaoa Baptista Borges, ya bayyana irin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Angola ta fuskar inganta amfani da makamshin da ake iya sabuntawa a kasar. A cewarsa, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar ta hada gwiwa da kamfanonin kasar Sin da dama a fannonin makamashi da ruwa, kuma a yanzu, an samu sakamako masu gamsarwa.
A cewar sanarwar da kamfanin Gezhouba wato CGGC na kasar Sin, wanda shi ne aka ba kwangilar aikin na Cacula Cabaca, an fasalta tashar ta yadda za ta samar da lantarki mai karfin megawatt 2,172. Kuma a yanzu haka, aikin ya samar da guraben ayyukan yi sama da 2,500, kuma daga cikinsu, kaso 81 ‘yan asalin yankin ne. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)