A kwanakin baya, yayin da shugaban kasar Burundi Evariste Ndayishimiye yake hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, ya bayyana cewa, alakar dake tsakanin Sin da Burundi tana da aminci da gaskiya, kasashen 2 sun sada zumunta tamkar ‘yan uwa. Ya ce, kasar Sin ba ta sanya wani hali na cin amana da tauye hali ba, kawa ce dake son tafiya tare da mu.
Kasar Sin ta samu ci gaba fiye da mu, amma kuma tana son hada kai tare da mu, da tafiya tare da mu kafada da kafada. Wannan ya sa yake da imani kan dangakatar dake tsakanin kasashen biyu, yanzu da kuma a nan gaba.
Shugaba Ndayishimiye ya yi farin ciki sosai kan yadda kofi da ti na kasar Burundi suka shiga kasuwar kasar Sin, da more damar da kasar Sin ta samar. Kana ya nuna godiya ga kasar Sin kan yadda ta samar da shinkafa irin na kasar Sin ga kasar Burundi, ta hakan kasar Burundi tana kusan cimma burinta na ganin dukkan ‘yan kasar sun samu abinci da kuma kudin ajiye.
Kana yana nuna amincewa sosai ga kasar Sin kan yadda ta koyar da fasahohinta da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, yana fatan za a kara sada zumunta da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Burundi a nan gaba. (Zainab)