Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da Wang Yi, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar, wanda ya kai ziyara a Paris na Faransa jiya Talata bisa agogon wurin.
Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar samun ci gaba mai inganci kuma ta inganta bude kofarta ga ketare, kana za ta ci gaba da bude kasuwarta ga kasashen duniya, ciki har da Faransa. Kasar Sin tana fatan bangaren Faransa zai iya samar da yanayin kasuwanci mai adalci ga kamfanoninta dake Faransa, tare da ba da gudummawarta ga ci gaban dangantakar Sin da kasashen Turai, da inganta amincewa da juna, ta yadda za a samu moriya tare.
A nasa bangare Macron ya bukaci Wang Yi da ya mika gaiwuwarsa ga shugaba Xi Jinping, inda ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar kalubaloli, Faransa tana son karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tare da bangaren Sin, ta yadda za su kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali tare. (Safiyah Ma)