A kwanakin baya, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya yi hira da wakilin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, inda ya jinjina wa shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da muhimminyar gudummawar da ya bayar domin tabbatar da ci gaban mata. Ya ce, shugaba Xi ya jagoranci gudanar da taron kolin mata na duniya na wannan karo, inda a lokacin aka waiwayi sakamakon da aka cimma a fannin neman ci gaban mata a duniya.
Shugaban na Ghana ya kara da cewa, a matsayin wurin da aka fitar da “Sanarwar Beijing”, kasar Sin ta cimma sakamako mai amfani a fannin bai wa mata karin iko, musamman ma kan wasu sabbin fannoni da suka hada da aikin sadarwa, da raya sabbin makamashi da dai sauransu. (Zainab Zhang)














