A kokarin shugaban hukumar NIS ta kasa na sake sauya fasalin al’amuran da suka shafi fasfo da samar da ingantaccen tsari, a ranar Asabar ya sake Æ™addamar da sabon ofishin fasfo a Auchi.
Bude sabon ofishin ya kara tabbatar da kudurin hukumar na bunkasa sashen samar da fasfon da inganta ta hukumar za ta yi gogayya da takwarorinta na duniya.
- NIS Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasa Zuba Jari A Nijeriya –CI James
- NIS Ta Ɗora Laifin Ƙarancin Fasfo A Kan CBN
A Jawabian shugaban hukumar, Isah Jere, yayin bude sabon ofishin ya ce, babu shakka samar da ofishin na da matukar muhimmanci wajen cimma aikin da aka dora masu na tabbatar da cewa an kusantar da tsarin bayar da fasfo ta yanar gizo ga jama’a.
Bayar da fasfo na zamani (e-Passport) ga ‘Yan Nijeriya na daya daga cikin muhimman ayyukan hukumar shige da fice t kasa.
A cikin shekarun da suka gabata an yi gyare-gyare sosai a tsarin bayar da fasfot a Nijeriya.
Tsarin fasfo na yanzu yana da mahimmanci sosai a yunƙurinmu na isar da shi ga ’yan Nijeriya kuma yana sake tabbatar da ƙudirin tabbatar da kyawawan ayyukan hukumar a idon duniya.
NIS na yin kokari don tabbatar da ƙarin buɗe ofisoshin a duk faɗin ƙasar don rage zirga-zirga.
Ya zuwa yanzu hukumar ta kaddamar da ofisoshin fasfo a garin Ilesha na jihar Osun da Daura a Katsina da Alimosho a Legas da Zaria a Kaduna da kuma garin Oyo na jihar Oyo.