Shugaban Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Felix Tshisekedi, ya kaddamar da cibiyar raya al’adu da kasar Sin ta ba da tallafin ginawa a birnin Kinshasa, fadar mulkin kasar.
Da yammacin jiya Asabar ne mista Tshisekedi, ya yanke kyallen dake alamta kaddamar da cibiyar, daga bisani kuma, yayin da yake kewaya sassan cibiyar, ya bayyana cewa, “Wannan aiki na hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Sin, na nuni ga hikimar sassan 2. Kaza lika, ana fatan cibiyar za ta bayar da damar cin cikakkiyar gajiya daga masana’antar raya al’adu, da sauya kasar zuwa muhimmiyar cibiyar kirkire-kirkire.”
A nasa tsokacin kuwa, ministan raya al’adu na kasar Faustin Elombe, cewa ya yi kammala aikin zai bude wani sabon babi na raya kirkire-kirkiren al’adu, da karfafa musayar su, da dunkule sassan kasashen Afirka.
Shi kuwa jakadan kasar Sin a kasar Zhao Bin, cewa ya yi aikin wanda sabon gini ne mai kayatarwa a Kinshasa, zai kara inganta masana’antar raya al’adun Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, tare da zama wani dandali mai muhimmanci, na baje kolin al’adun gargajiyar kasar. (Saminu Alhassan)