Shugaban Karamar Hukumar Koko/Bese da ke Jihar Kebbi, Yahaya Bello, ya ba da umarnin rufe wani otal mai suna ‘White House Hotel’ da ke yankin Koko bisa samun rahoton gudanar da haramtattun harkarla da suka hada da sayar da giya da kuma yin karuwanci a otal din.
Shugaban ya bada umarnin a jiya sa’ilin da ke ganawa da ‘yan jarida a yankin Koko inda ya ce dole su tsarkake yankin daga wadannan munanan dabi’un.
- Zan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Kamar Yadda Buhari Ya Yi – TinubuÂ
- Sin Ta Yi Rawar Gani Wajen Tallafawa Ayyukan Daidaita Sauyin Yanayi
“Wannan otel din ya zama wani dandamali kuma maboyar mata da matasa inda suke aikata ashsha da muggan dabi’u na manya laifuka.
“Sannan wurin ya zama barazana Kuma abun kunya wajen rayuwa, musamman ga al’ummomin yankin kana yana kawo cikas da nakasu ga harkokin kasuwanci inda suke aikata ashshansu cikin dare”.
Bello ya yi kira ga al’ummar Koko da suke Kai rahoton faruwar duk wasu ayyukan ashsha ga hukumomin tsaro domin daukan matakan da suka dace.
Wakilinmu ya shaido mana cewar tunin jami’an tsaro suka dukufa wajen tabbatar da doka da oda da kare al’ummar yankin.