Mummunar ambaliyar ruwa a Jihar Bayelsa ta mamayi kauyen Otuoke da ke karamar hukumar Ogbia, inda hakan ya janyo nutsewar gidaje, coci da yawa da gonakai da dama.
A wani ziyarar da aka kai jiya zuwa yankin ta cikin Jirgin Ruwa mai kansa, sama da kashi 80 cikin dari na gidaje a yankin ne ambaliyar ta shafa ciki kuwa har da gidan tsohon Shugaban Kasa, Dakta Goodluck Jonathan.
- Shugaban Karamar Hukuma Ya Rufe Otal Kan Aikata Ayyukan Badala A Kebbi
- Taron Wakilan Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Na 20 Da Muhimmancinsa
Bayan wannan ma, a shekarar 2012 lokacin da Jonathan ya ke mulki, an taba samun ruwan ta mamaye gidansa da ke Otuoke.
Talla
Sauran yankunan da ruwan ya barnata sun hada da cikin jami’ar Otuoke, cocin Anglican, cibiyar lafiya da asibiti da sauran wuraren.
Talla